1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kolin kungiyyar Au a Libya

Ibrahim SaniDecember 30, 2005

Shugabannin kungiyyar tarayyar Africa zassu gudanar da taron kolin su a Libya, makonni uku kafin babban taron kungiyyar a Sudan

https://p.dw.com/p/Bu2r
Cif Obasanjo na Nigeria
Cif Obasanjo na NigeriaHoto: dpa

A lokacin wannan taron koli, an shirya cewa shugabannin wasu kasashe a nahiyar ta Africa takwas ne zasu hallara a kasar ta Libya, a ranar hudu ga watan Janairu, don tattauna batutuwa da suka shafi yankin Darfur na kasar Sudan a hannu daya kuma da dangantakar da tayi tsami a tsakanin kasar Sudan da kuma Chadi.

Ana sa ran cewa a lokacin wannan taro shugabannin na Africa zasu samo bakin zaren kara kaimi ga wakilan taron sulhun warware rikicin yankin Darfur, a tsakanin kungiyoyin yan tawaye da kuma bangaren gwamnati da yanzu haka keci gaba da gudana a birnin Abujan tarayyar Nigeria.

Idan dai an iya tunawa, an sha gudanar da tarurruka iri daban daban a game da warrware wannan rikici na yankin na Darfur na kusan tsawon watanni talatin, amma ina kamar an shuka dusa.

A cewar kwamishinan sulhu da tsaro na kungiyyar ta Au, wato Said Djinnit,shugabannin na Au zasu sa kaimi ga wakilan wannan taro na ganin cewa a wannan karo kwalliya ta biya kudin sabulu.

Tuni dai wasu jami´ai na Amurka suka bayyana fatan su na ganin cewa an samo bakin zaren warware wannan rikici na yankin na Darfur a karshen shekarar nan ta 2005 mai karewa.

Bugu da kari rahotanni sun kuma shaidar da cewa shugabannin na Africa sun kuma damu kwarai matuka, a game da yadda dangantaka a tsakanin kasar Sudan da Chad take ci gaba da tabarbarewa, a sakamakon zargi da kasar ta Chad tayiwa sudan da cewa tana daurewa kungiyar yan tawaye na kasar gindi a kokarin da suke na kifar da gwamnatin kasar ta Chadi,karkashin shugabancin Idris Debby.

Idan dai an an tuna, a kusan makonni biyu da suka gabata,anyi wata arangama a tsakanin dakarun gwamnatin ta Chadi da wasu mambobin kungiyyar yan tawayen kasar a can garin Adare, wanda hakan yayi sanadiyyar salwantar rayuka sama da dari.

A bayan wannan arangamar ne kuma, kungiyyar yan tawayen ta Chadi tayi kurarin kai wani harin a birnin Djemaina, tare da tabbatar da cewa tana yin hakan ne don kifar da gwamnatin kasar ta Chadi.

Rahotanni sun shaidar da cewa wadannan batutuwa biyu na daga cikin muhimman abubuwa da wannan taron kolin zai tattauna a kann su a lokacin taron kolin na kasar ta Libya.

Bugu da kari bayanan sun kuma tabbatar da cewa daga cikin shugabannin kasashen da zasu halarci wannan taro sun hadar da Nigeria da Sudan da Eritrea da Masar da kuma kasar Africa ta tsakiya.

Ragowar shugabannin kasashen sun hadar da mai masaukin baki wato Libya da chadi da kuma Gabon.

Wannan taro dai an nunar da cewa za a gudanar dashi ne makonni uku kafin fara gudanar da babban taron kolin kungiyyar ta Au a can birnin Khartoum na kasar Sudan.