1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kolin kungiyyar ciniki ta duniya a lardin Hongkong

December 13, 2005
https://p.dw.com/p/BvGb

Ministocin harkokin ciniki na kasashe kusan 150 na duniya na naci gaba da gudanar da taron kolin su na kwanaki shida a lardin Hongkong dake kasar Sin.

Babbar ajanda dake gaban wannan taro dai shine na samo bakin zaren warware irin banbance banbance dake akwai ne ta fannin ciniki da kasuwanci a tsakanin kasashe masu tasowa da kuma takwarorin su masu ci gaban masana´antu na duniya.

A cewar bayanai da suka iso mana, mahalarta taron zasu gudanar da tattaunawar tasu ne game da matakan dake kunshe cikin batutuwan tattaunawar birnin Doha,wanda a wancan lokaci aka tashi daga taron ba tare da an cimma wata matsaya guda ba.

Korafe korafen kasashe masu tasowar dai shine na bukatar ganin an cire duk wasu sarkafe sarkafe dake akwai a harkokin gudanar da ciniki da kuma kasuwancin.

A waje daya kuma, rahotanni sun nunar da cewa , masu adawa da hadewar tattalin arziki guri guda, arangama suka yi da jamian tsaro a kusa da inda wannan taro yake gudana.