1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kolin shugabannin kasashen kungiyar tarayyar Turai a birnin Brussels.

Mohammad Nasiru AwalMarch 25, 2004
https://p.dw.com/p/Bvl4

Bisa al´ada taron kolin farkon shekara na kungiyar Tarayyar Turai ya fi mayar da hankali akan batutuwan da suka shafi tattalin arziki, to amma a wannan karon batun yaki da ayyukan ta´addanci na kasa da kasa shine ya fi daukar hankalin dukkan mahalarta taron. Dalilin haka kuwa shine hare-haren ta´addancin da aka kaiwa birnin Madrid na kasar Spain a ran 11 ga wannan wata na maris, wanda ya kada nahyiar Turai baki daya. Don mayar da martani ga wadannan hare-haren shugabannin gwamnatoci da na kasashen kungiyar tarayyar Turai dake halartar wannan taron kolin, sun kuduri aniyar daukar sahihan matakai da nufin kyautata hadin kai tsakaninsu, musamman wajen masuyar bayanai tsakanin jami´an ´yan sanda da na tsaro da kuma hukumomin leken asiri na kasahen kungiyar ta EU. Yanzu haka dai majalisar zartaswan kungiyar ta amince da kirkiro wani mukami na jami´in kula tare da ba da shawarwari dangane da matakan yaki da ta´addanci da dukkan kasashen kungiyar ke dauka. A cikin makon jiya wani taron ministocin harkokin cikin gida na kasashen kungiyar EU ya ba da shawarar kirkiro wannan mukami don yakar ´yan ta´adda a Turai.

Wani batu da ke kan ajandar taron kolin shine game da kundin tsarin mulkin kungiyar EU bayan an fadada ta a ran daya ga watan mayu. Yanzu haka dai an fara ganin kyawawan almun cewa za´a cimma daidaito dangane da kundin tsarin mulkin, bayan da kasar Poland, wadda ta ke nuna adawa da wasu sassa wannan tsarin mulki, ta sassauto daga matsayin ta na farko. Ita ma sabuwar gwamnatin kasar Spain karkashin jagorancin Jose Luis Rodriguez Zapatero na jam´iyar Social-Democrats ta ce a shirye ta ke ta albarkaci sabon kundin tsarin mulkin. Abin da ake takaddama akai dai shine batun yawan kuri´u da za´a ba kowace kasa bisa la´akari da yawan al´umarta. Hakan dai ka iya rage tasirin da kasashen Poland da Spain zasu samu a cikin kungiyar ta EU.

Wani batu na gaba da shugabannin kasashen na EU zasu tattauna akai shine game da halin da ake ciki a yankin GTT, da zummar gano irin rawar da ita ma kungiyar EU din zata taka wajen samar da zaman lafiyar a wannan yanki dake fama da rikici.

A karshe shugabannin na Turai zasu shawarta game da sauye-sauyen tattalin arziki. Yau dai shekaru hudu kenan tun bayan taron birnin Lisbon, inda shugabannin kungiyar EU suka kuduri aniyar daukar sahihan matakai don mayar da yankinsu zama ja gaba a karfin tattalin arziki cikin shekaru 10. To amma har yanzu ba bu wata alamar cimma wannan buri, saboda matsalolin kudi da na yawan marasa aikin yi da ake fuskanta a Turai.