1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Komitin Sulhu a game da harin Isra´ila a Kana

July 30, 2006
https://p.dw.com/p/Buob

Komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia ya gudanar da taron gaggawa game da harin da Isra´ila ta kai yau agarin Kana na kudancin Labanon, wanda kuma yayi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 50, mafi yawan su mata da kanaan yara.

A jawabin da yayi ga taron na komitin Sulhu, Sakatare jannar Kofi Annan, ya nuna matuƙar ɓacin rai ga wannan hari.

A nasa gefe jikadan Isra´ila a komitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia, Dan Gillerman ya ce ƙasar sa,ta ji takaici wannan kuskure, to saidai tsuntsun da ya jawo ruwa, shi ruwa ke duka.

Jim kaɗan, bayan abkuwar harin Kasashe da kungiyoyin daban-daban na dunia sun yi ta tofin Allah tsine, ga Isra` ila wasu kuma sun shirya zanga-zanga.

A nata ɓangare, ƙasar Iran, ta yi kira ga dakarun ta, da al´ummomin ta, su kwan da shirin yaƙar Isra´ila.