1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron komitin tsaron AU a Addis Abeba

Yahouza S.MadobiOctober 17, 2006

Shugabanin ƙasashe membobin komitin tsaron AU sun buɗa zaman taro, a game da rikicin Côte d´Ivoire.

https://p.dw.com/p/Btxj

Komitin tsaro na ƙungiyar gamayyar Afrika, ya ƙaddamar da wani mahimmin zaman taro, a cibiyar AU, da ke birnin Addis Abeba na ƙasar Ethiopia, da zumar lalubo hanyoyin warware rikicin ƙasar Cote d´Ivoire.

Daga shugabanin ƙasashe 15, da ke matsayin membobi a komitin tsaron ƙungiyar gamaya Afrika, a ƙalla 8 su ka halarci taron na Addis Abeba, wanda su ka haɗa da shugaban ƙungiyar AU, Denis Sasso Nguesso, da shugaban Burkina Faso ,Blaise Campaore, da na Senegal Abdoulaye Wade, da Omar Bango na Gabon.

Shugaba Lauran Bagbo na Cote d´Ivoire, da Praminstan riƙwan ƙwarya Charles Konnan Banny, na daga cikin mahalarta wannan taro, saidai yan tawayen Forces Nouvelles, da ke riƙe da arewancin Ivory Coas,t sun ƙaurace masa.

Komitin tsaron AU, na tantanawa a game da hanyoyin hidda Cote d´Ivoire ,daga rikicin tawaye da na siyasa, da ta tsinci kanta ciki, tun shekaru 4 da su ka gabata.

Mahalarta taron su yi nazari a kann shawarwarin da ƙungiyar ECOWAS ko kluma CEDEAO,ta bayar, a zaman taron da ta yi a birnin Abujan Nigeria, ranar 6 ga watan da mu ke ciki.

Magabatan ECOWAS, sun bada shawara, shugaban Lauran Bagbo, ya ci gaba da riƙe ragamar mulki nan da shekara guda, kamin gudanar da zaɓe.

Saidai a ɗaya hannun CEDEAO ta buƙaci damƙawa Praminsita jagorancin rundunar tsaro ta ƙasa,domin a halin yanzu, mulkin sa na da matuƙar rauni, dalili da rashin dogaro madafar soja.

Bugu da ƙari CEDEAO, ta bada shawara gaggauta kwance ɗamara yaƙi ga yan tawaye, da sojojin sa kai, masu nuna goya baya, ga shugaba Lauran Bagbo.

Shugabanin ƙasashen komitin tsaron ƙungiyar gamayya Afrika, sun yi masanyar ra´y oyi, a game da batun shiga tsakani, da shugaban ƙasar Afrika ta kudu Tabon Mbeki ke yi, a rikicin Cote d´Ivoire.

Idan dai ba a manta ba, yan tawaye da jam´iyun adawa, sun zargi Mbeki, da nuna sa rai, ga ɓangaren shugaba Bagbo.

Bayan nazari da ya gudanar, komitin tsaron AU, za shi gabatar da shawarwarin da ya yanke, ga Majalisar Dinkin Dunia, ranar 25 ga watan da mu ke ciki, wadda zata ɗauki matakin da ya dace.

Tun dai ranar asabar da ta wuce, Majalisar Dinkin Dunia, ta hiddo sanarwa, inda ta ce, ba za yiwu ba, a shirya zaɓe ranar 31 ga watan oktober a Cote d Ivoire, kamar yadda a ka tsara da farko, sannan Majalisar, ta ƙara wa´adin shekara guda.

Masu bin diddiƙin rikicin Cote d´Ivoire, sun nunar da cewa, taron na Addis Abeba, ba zai barkata komai ba, wajen warware wannan rikici, ƙaurace masa, da yan tawaye su ka yi, na ɗaya daga alamomin da ke nuni da hakan.