1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kungiyar ƙasashen musulmi ta duniya

August 1, 2006
https://p.dw.com/p/BuoE

ƙungiyar ƙasashen musulmi ta duniya ta ce zata matsa ƙaimi wajen ganin an sami tsagaita wuta a Lebanon ba tare da wani sharaɗi ba. Ministan harkokin wajen Malaysia yace ƙungiyar zata gudanar da taro a Malaysian a cikin wannan makon. P/M ƙasar Malaysia Abdullahi Ahmed Badawi wanda ke shugabantar ƙungiyar a yanzu ya yi kiran gudanar da taron a ranar Alhamis mai zuwa. Taron zai kuma buƙaci sanya sojojin ƙasashen musulmi cikin rundunar sojin gamaiyar ƙasa da ƙasa ta kiyaye zaman lafiya da majalisar dinkin duniya ke shirin turawa zuwa Lebanon. Jigon taron dai shi ne tattauna halin da ake ciki a Lebanon da kuma yankin Palasdinawa. Ƙasashen Masar da Iran da Syria na daga cikin ƙasashe goma sha takwas da zasu halarci taron.