1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kungiyar AU a Addis Ababa

March 10, 2006

Kungiyar AU na taro akan tsaron zaman lafiyar Darfur

https://p.dw.com/p/Bu1C

Tun abin da ya kama daga watan fabarairu na shekara ta 2003 ne ake fama da yakin basasa a lardin Darfur, wanda yayi sanadiyyar rayukan mutane sama da dubu 300 sannan wasu miliyan biyu da rabi kuma suka tagayyara a sansanonin ‘yan gudun hijira, kamar yadda alkaluma na MDD suka nunar. Su kuma sojojin kiyaye zaman lafiya da kungiyar tarayyar Afurka ta tsugunar a can tun a shekara ta 2004 suna fama da wahala saboda rashin nagartattun kayan aiki. A lokacin da yake bayani game da haka shugaban kungiyar Alpha Konare cewa yayi:

“A hakika mun san makurarmu. Aikin kiyaye zaman lafiya ba alhaki ba ne da ya rataya a wuyan kungiyar tarayyar Afurka, muhimmin abin da ta sa gaba shi ne matakai na riga kafin billar rikici da kuma shawo kan matsalolin dake akwai a cikin gaggawa. Rikicin Darfur ya ci gaba da yin tsamari ne saboda mun kasa samun bakin zaren warware matsalar a siyasance. Kuma ba tare da la’akari da shawarar da za a tsayar ba, tilas ne a lura da wasu abubuwa guda biyu..da farko wajibi ne Kungiyar Tarayyar Afurka ta zama ja-gaba, sannan na biyu kuma wajibi ne a girmama ikon cin gashin kan kasar Suda.”

Halin da ake ciki a lardin na Darfur mai fama da rikici dai sai dada tabarbarewa yake yi. A sakamakon fadan da ake ci gaba da gwabzawa da hare-haren ba zata da ake fuskanta al’amuran taimako ga mutane miliyan uku da rabi dake yankin yanzu haka ya ta’azzara. Wani abin mamaki a nan kuwa shi ne yadda Amurka ke ba wa Kofi annan goyan baya a game da lalle sai an tura sojan kiyaye zaman lafiya na MDD zuwa yankin na Darfur. Mai yiwuwa hakan ne ya sanya Sudan din take ta da kayar baya, inda aka ji ministan tsaron kasar Abderrahim Hussein yana mai fadin cewar:

“Darfur zata zama makabarta ga dukkan masu katsalandan da shisshigi. Wannan shi ne sakon da muke aika wa duniya. Sojojinmu da dakarun sa kai da sauran al’umar kasa, dukkansu a shirye yake su kare makomar kasar Sudan.”

Bisa ga ra’ayin Alpha Konare dai muddin gwamnatin Sudan ta ci gaba da dagewa akan matsayinta na kin amincewa da rundunar tsaro ta MDD da wuya a cimma biyan bukata. Ya kuma kara da cewar:

“Tilas ne a ba wa nahiyar Afurka fifiko wajen sasanta matsalolinta na cikin gida. Ko shakka babu muna bukatar hadin kai daga MDD, amma da farko wajibi ne a fara dora wa nahiyar alhakin warware matsalolinta. Wani abin da su kuma shuagabannin Afurka ya kamata su fahimta shi ne tilas ne su rungumi alhakin da ya rataya wuyansu su tashi tsaye wajen warware matsalolinsu a maimakon maganganu na fatar baki kawai. Muddin ba su dawo daga wannan mummunar dabi’a ba to kuwa da wuya su samu kafar shawo kan rikice-rikice na nahiyar.”

A dai halin da ake ciki yanzu Alpha Konare ya ba da shawararsa ga Kungiyar ta AU, amma shawara ta karshe ta rage a hannun kwamitin tsaro da zaman lafiya na kungiyar ko da yake Sudan ta amince da a bunkasa yawan rundunar kiyaye zaman lafiya daga dubu 7 a yanzun zuwa dubu 10, dangane da sojan MDD kuwa ministan harkokin wajen Sudan Lam Akol ya ce sai nan gaba za a tsayar da wannan shawo