1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kungiyar AU a Ghana

July 1, 2007
https://p.dw.com/p/BuHQ

A yau ne shugabannin kasashen tarayyar Afrika suka bude taron yini uku a birnin Accra,Ghana ,wanda keda nufin kawo hadin kai tsakanin wakilan ta,ganin cewa akwai cigaba dangane da harkokin shugabanci a nahiyar.

Shugaban gudanarwa na kungiyar Alpha Oumar Konare,ya bude taron na yini uku da bayanai dangane da da halin da kungiyar take ciki,tare da kira ga mdd data tursasawa Sudan wajen amincewa da dakarun hadin gwiwa da ake shirin aikewa lardin Darfur mai fama da rigingimu.Buguda kari yayi amfani da wannan dama wajen kira ga shugabbanin kashe 53 dake wannan nahiya mafi talauci,dasu sake tunani dangane da yadda zasu farfado da kasashensu.Omar Konare yace dole ne su dada zage dantse wajen ganin cewa an samu sauyi na cigaba a kowane bangare na Afrika.