1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kungiyar cinikaiya ta duniya a Geneva

July 1, 2006
https://p.dw.com/p/Bus8

A gun taro kan harkokin kasuwancin duniya a birnin Geneva, shugaban kungiyar cinikaiya ta duniya WTO, wato Pascal Lamy ya yi gargadi game da wani rikici idan ba´a samu wani ci-gaba akan batun tallafin da ake ba wa manoma ba. Lamy ya fadawa wakilan kasashe 149 membobin kungiyar WTO cewa idan ba´a cimma daidaito ba to hakan zai raunana kungiyar da kuma tsarin cinikaiya na duniya baki daya. Manyan kasashen dake halartar taron wato Amirka da KTT na kai ruwa rana game da yawan tallafin aikin noma da zasu janye don samun sukunin taimakawa kasashe masu tasowa. A karshen wannan shekara zagayen tattaunawar da ake yi yanzu wanda ake yiwa lakabi da tattaunwar Doha, yake karewa.