1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kungiyar ciniki ta duniya akan yarjejeniyar ciniki ta duniya.

Hauwa Abubakar AjejeOctober 12, 2005

An kammala taron ba tare da baki ya zo daya akan batun yanke harajin anfanin gona ba,da yake mafi muhimmanci a gaban taron

https://p.dw.com/p/BvYq
Hoto: AP

Wata majiya ta diplomasiya tace,ministocin na Kungiyar Taraiyar Turai,Amurka,Brazil,India,da Australia,wadanda suke kokarin ganin an cimma yarjejeniya akan musamman kasuwanci na albarkatun gona,zasu sake ganawa ranakun laraba da alhamis na mako mai zuwa a birnin Geneva.

Kungiyar taraiyar Turai ta samu kanta karkashin matsin lamba na sauran kasashe domin ta amince da rage wasu shingaye na shigowa da kayan anfanin gona,bayan Amurka ta alkawarta rage kudaden haraji na anfanin gonarta.

Kungiyar cinikin mai membobi 148 tana bukatar samarda shawarwari da zata mikawa taronta da zaa gudanar a Hong Kong a watan disamba mai zuwa,kodayake har yanzu suna ci gaba da tattauna wasu batutuwa musamman batun anfanin gonan da ya shige musu gaba.

Rashin samun daidaito akan wannan batu, zai zama cikas ga taron,wanda samun nasararsa zai habaka tattling arzikin duniya da biliyoyin daloli, ya kuma taimaka kubutar da daruruwan miliyoyin mutane daga kagin talauci.

Cikin wani rahoton wata kungiyar mai zaman kanta tace,yarjejeniyar da taron kungiyar ciniki ta duniya take niyyar cimmawa zai taimakawa dukkanin kasashe sai dai wasu kasashe kadai masu tasowa,yawancinsu daga nahiyar Afrika.

Bayan watanni na taruka irin wannan da ministocin suka gudanar a baya, da alamun cewa taron na baya bayan nan,ya doshi cimma yarjejeniya da ake bukata,inda Amurka ta yi tayin rage kashi 60 cikin dari na harajin kayayikin abincinta.

Sai dai kuma ba nan gizo ke saka ba,domin kasar Amurka da Kungiyar Taraiyar Turai,wadanda manomansu suke cikin wadanda suke da mafi kariya a duniya,suna fuskantar bukatu iri dabam dabam daga abokan huldarsu na ciniki,da su ke neman Karin sassauci,a daya hannun kuma matsaloli daga wasu daga gundumominsu da suke bukatar rage sassauci da ake da shi yanzu.

Ministan harkokin wajen kasar Brazil Celso Amorim da sauran shugabannin kasashe nasu tasowa, sun baiyana tsoronsu game da tayin da Amurka tayi inda suke ganin cewa ba zata ainihin yanke harajin ba yadda ake bukata inda ya bukaci a faiyace fannonin da zaayi ragin da kuma yadda zaayi.

Duk da haka masu nazari da kuma masu saisaita ciniki sunce yanzu hankula sun juya kan kungiyar taraiyar turai,saboda a cewarsu, idan baa samu sassauci a cikin harkokin kasuwancin da ya shafi anfanin gona ba,ba zaa samu kafar cimma yarjejeniya ba a taron nasu na Hong Kong.

Muddin dai baa samu baki ya zo daya akan batun harajin ba,Amurka tace ba zata mika batun tayin nata a gaban majalisa ba,yayinda kuma manyan kasashe masu tasowa kamar Brazil,tace, ba zata iya bude kasuwanninta ga albarkatun masanaantu ba,wanda yake daya daga cikin batutuwa da ake son tattaunawa kansu.