1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kungiyar ciniki ta duniya

Hauwa Abubakar AjejeDecember 13, 2005

Taron yana kokarin mayarda hankali akan taimakawa kasashe masu tasowa tare da nufin sassauta haraji akan kayaiyakinsu

https://p.dw.com/p/Bu3Q
Pascal Lamy Darekta Janar Kungiyar Ciniki ta Duniya
Pascal Lamy Darekta Janar Kungiyar Ciniki ta DuniyaHoto: dpa

Yayinda kasashen Amurka,kasashen Kungiyar Taraiyar Turai da manyan kasashe masu tasowa kamar Brazil da India suke tattaunawa akan hanyoyin inganta kasuwanci,batun wani shiri na musamman ga kasashe masu tasowa yana neman mamaye taron na yau.

Komishinan ciniki na kungiyar taraiyar turai, Peter Mandelson yace yana son ganin batun kara taimako ga kasashe masu tasowa ya zama shine muhimmi a gaban taron na kwanaki 6.

Shima wakilin kasar Amurka Rob Portman,ya goyi bayan wannan batu,ya kara da cewa kamata yayi taron ya bullo da hanyoyi na musamman na huldar kasuwanci da zasu taimakawa kasashe masu tasowa.

Taron kungiyar a Doha,a 2001 ya shawarta kawarda dukkan shingaye na kasuwanci tare da kuma bukatar yin anfani da wasu hanyoyi na musamman da zasu taimaka wajen kasuwanci da kasashe masu tasowa,sai dai an samu cikas wajen kaddamar da wadannan shirye shirye saboda takaddama da ta taso kan harkokin aikin gona cikin kungiyar.

An dai zargi kasashe masu arziki da laifin rashin sassauta manufofin ciniki da kuma rage goyon baya da suke baiwa manomansu,wanda ake ganin yake hana ruwa gudu a harkokin kasuwanci tare da kashe kasuwar manoman kasashe masu tasowa.

A halin yanzu dai membobin kingiyar suna kokarin ganin basu fada cikin rikici da ya taso a lokacin taronsu a 2003 ba,musamman kan anfanin gona wanda ya iza wutar rushewara taron.

Jamian a sunce,taron zai iya mayarda hankali akan tayin kungiyar taraiyar turai ta tattauna batun kawadda haraji kan ko wace irin haja amma banda makamai ga kasashe masu tasowa.

Hakazalika kasar Amurka ta zo da nata shiri da ya mayarda hankali akan Afrika, kasar Japan kuma a kwanan nan ta sanar da shirin bada gudumowar dala biliyan 10 domin habaka fitar da hajoji daga kasashe matalauta zuwa kasashe masu karfin masanaantu.

Kasashe masu tasowa dai cikin kungiyar,basa aiki tare a matsayin kungiya, a taron na kungiyar ciniki ta duniya haka kuma a yawancin lokuta ana samun gasa tsakanin kasashe masu arziki da suke da wata shaawa ta musamman akan harkokin kasuwanci da daya daga cikin kasashen masu tasowa.

Sai dai ministan ciniki na kasar India Kamal Nath,yayi gargadin hana duk wani yunkuri na kawo farraga ta hanyar bada taimako ga wasu kasashe a bar wasu.

Cikin sako da ya aika wajen taron,sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan,yace yana fatar kasashen kungiyar ta ciniki zasu yi iyaka kokarinsu na ganin sun bullo da hanyoyin da zasu kawadda talauci cikin miliyoyin jamaar kasashe masu tasowa.

Ana dai sa ran cewa taron na Hong Kong,zai samarda muhimmin mataki na karshe na samarda yarjejeniya akan shawarwarin taron Doha,wanda aka kaddamar shekaru 4 da suka shige a Qatar tare da nufin fitar da miliyoyin mutane a kasashe masu tasowa daga kangin talauci ta hanyar bunkasa kasuwanci.