1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Kungiyar gamayyar Afrika

Zainab A MohammadJanuary 28, 2007

A gobe ne shugabbanin kasashen kungiyar gamayyar Afrika Au ke bude taro a birnin Adisa baban kasar Habash,taron da ake ganin zai fuskanci

https://p.dw.com/p/BtwU

sabanin raayin adangane da kasar da zata karbi shugabancin wannan kungiya mai wakilan kasashe 53.

Gabannin bude wannan taro dai an jibge jamian tsaro a fadar gwamnatin habashan,daga titi zuwa titi,domin kare lafiyar masu halartan taron da suka hadar da manyan jakadun kasashe da sakatare general na mdd Ban Ki Moon.

Wannan taron na yini biyu wanda ke zama na Takwas din irinsa da kungiyar ta AU ta gudanar,zai tattauna batutuwan da suka hadar da tura ayarin sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa kasar Somalia dake fama da rikicin sojin sakai,da matsaloli dake tattare da dumamar yanayi da duniya ke fama dashi.

To sai dai daura da wadannasn matsaloli akwai kuma matsalar cimma yarjejeniya kann lardin Darfur,da kuma yunkurin Sudan din na karbar ragfamar shugabancin wannan kungiya.Tun a bara nedai Sudan ta gaza samun wannan matsaya sakamakon rasdhin cimma matsaya guda kann Lardin na Darfur.

Ayayinda jamian agaji ke dada kokawa da yadda lamura ke dada rincabewa a Darfur ,duk dacewa ministan harkokin sudamn Lam Akol yace kasarsa a shirye take ta karbi kujerar shugabancin kunguiyar ta AU. Mr Akol wanda ke halartan wannan tarton na Adisa baba ya fadawa manema labasru cewa,bawa Sudan wannan shugabanci zai kasance abu mai kyau wa kungiyar,

To sai dai da kaddamar da wannan taro a safiyar yauz,bisa dukkan alamu zaa fuskanci matsaloli ,inda tuni Chadi tayi barazanar shure taron,idan har aka zabi sudan ta jagoranci wannan kungiya.

shugabanci dai shine batu na farko da taron zai fara muhawara akai,kuma kowane irin lokaci aka bata akan hakan,zai kawo cikas ne kadai wajen tattauna sauran batutuwa.Sakatare general na mdd Mr Ban ki Monn wanda zai gana da shugaba Hassan Omar Elbashir na sudan a wajen taron,a makon daya gabata ya bayyana damuwansa adangane da harin boma bomai da dakarun sojin gwamnatin kasar suka kai a yankunan arewacin Sudan din.

Bugu da kari a wata sanarwar daya gabatar a wurin taron,Archbishop Desmond Tutu na kasar Afrika ta kudu yayi kira ga kungiyar ta Au dasu bayyana rashin jin dadinsu da halinda ake ciki a Sudan.Majiya daga taron dai na nuni dacewa kungiyoyin kare hakkin jamaa da dama sun soki bawa Sudan wannan zagaye na shugabanci,duk dacewa itace kadai ta gabatar da wannan muradi.