1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Kungiyar Musulmi ta OIC a Saudi Arabia

December 7, 2005
https://p.dw.com/p/BvHa

Yau ne a kasar Saudiyya, a ka buda taron shugabanin kasashe da sarakuna na kungiyar musulmi ta dunia, wato OIC ko kuma OCI, bisa jagorancin Sarki Abdalah mai masabkin baki.

A cikin jawabin sa na bude taron, Sarki Abdallah ,ya yi kira ga musulmi na dunia, da su daina bata sunan addinin islama ta hanyar hare haren ta´adanci da su ke kaiwa da sunan addini.

Ya yi suka da kakkausar halshe da yan tsautsauran ra´ayi, da ke kiran su yan kishi addinin Islama.

Lokaci yayi, inji sarki Abdallah na kasashen musulmi na dunia su hada kai, domin fuskantar kalubele da barazana da makiya addini ke nuna masu.

Kazalika, ya bukaci kasashen musulunci ,sun yi kwaskwarima ga tsarin bayar da illimi cikin makarantu, ta yadda illimin da matasa ke samu, ya yi daidai da umurnin zaman lahia, tubali tushe na girkuwar addinin musuluci.

A bangaren yaki da talauci , jawabin na Sarki Abdallah,ya gayyaci shugabanin kasashen musulmi ,da su yi koyi da akidar addinin musulunci, ta taussayi da cude ni, in cude ka ,tsakanin al´umma.

A karshe wannan taro, gobe idan Allah ya kai mu , za a gabatar da sanarwar hadin gwiwa, a kan pasalin cimma burin hadin kan kasashen musulmi, nan da shekaru 10 masu zuwa.