1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

TARON KUNGIYYAR AU A HABASHA.

July 6, 2004
https://p.dw.com/p/BviO

Sakataren mdd Kofi anan ya bukaci shugabannin kasashen nahiyar Africa dasu taimaka wajen ganin an samu wanzuwar zaman lafiya a yankin Dafur n a kasar Sudan.

Kofi Anan ya fadi hakan ne yayin da yake jawabi a gaban taron kolin kungiyyar a yau talata a can birnin addis Ababa na kasar Habasha.

Babban sakataren mdd ya tabbatar da cewa rikicin yankin Dafur na kasar sudan abune dake bukatar taimakon gaggawa wanda idan ba ayi hankali ba ka iya haifar da wani sabon rikicin izuwa wasu kasashe dake makotaka da kasar ta Sudan.

Bugu da kari Kofi anan ya kuma tabbatar da cewa wan nan rikici na yankin na Dafur a yanzu haka na a matsayin wata baraza na ga kokarin da kasashen nahiyar ta African keyi game da yaki da matsalolin cututtuka da yunwa da kuma fatara.

Rahotanni daui sun nunar da cewa a yanzu haka wan nan rikici na ya nkin na Dafur na a matsayin zakaran gwajin dafi ga kungiyyar ta Au a matsayin ta na kungiyya dake warware rikice rikice dake faruwa a wasu kasashe mambobi a cikin ta.

Ya zuwa yanzu dai majiya mai karfi daga kungiyyar ta Au ta tabbatar da cewa tuni ta cimma yarjejeniyar aikewa da dakarun kiyaye zaman lafiya daga tarayyar Nigeria da kasar rwanda izuwa yankin na dafur karkashin lemar kungiyyar don gudanar da aikin tabbatar da tsaro da kuma kare dukiyoyin alummar yankin baki daya.

A wata sabuwa kuma yayin da shugaban kungiyyar mai barin gadom,wato Mr Chissano ke yin jawabin sa na ban kwana an fuskanci rashin gane takamaimai mai yake cewa bisa amfani da harshen kisuahili da yayi a maimakon harsuna uku da aka yarda dasu wato Ingilishi da faransanci da kuma larabci.

Mr Chissano ya tabbatar da cewa yayi amfani da harshen kisuahilin ne don fito da aladu da kuma dabiun yan Africa wanda hakan na daya daga cikin aikin kungiyyar ta Au.

Jim kadan bayan kammala jawabin nasa jakadan kasar Sudan a habasha ya mike tsaye ya sanarwa da duniya cewa sabon shugaban kungiyyar na gaba bayan saukar Mr Chissano shine shugaban tarayyar Nigeria wato Olesegun Obasanjo,wanda inji shi shi kuma zaiyi nasa bayanin ne a nan gaba cikin harshen larabci.

A waje daya kuma bayanai daga birnin na addis Ababa sun shaidar da cewa kasashen Libya da Habasha na nan na karamniya na neman ganin babban ofishin kungiyyar na Eu ya zauna a kasashen nasu.

Rahotanni dai sun tabbatar da cewa don ganin wan nan buri nata ya cika tuni kasar ta habasha tayi alkawarin bada fili kyauta don tsugunar da kungiyyar ta Eu da kudin sa yai dalar Amurka miliyan 50.

Ita kuwa kasar Libya cewa tayi zata bawa dukkkannin jamian kungiyyar da zasu yi aiki a hedikwatar gidaje don zama kyauta ba tare da b iyan ko sisi ba.

Ana dai kyautata zaton cewa wan nan takaddama na daga cikin ajandar da taron kolin zai mayar da hankali a kai a lokacin tattauna mihimman batutuwa a ragowar kwanakin da suka rage na gudanar da wan nan taro.

Ibrahim sani.