1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron mahhali a Majalisar Ɗinkin Dunia

September 25, 2007
https://p.dw.com/p/BuAL

A birnin New York na ƙasar Amurika, an kawo ƙarshen taron ƙoli a game da neman matakan yami da ɗumamar yanayi.

Sakatare Janar an Majalisar Ɗinkin Dunia Ban Ki Moon, da ya jagoranci wannan taro ya bayana matuƙar gamsuwa da haɗin kan ƙasashen dunia, a game da wannan batu.

A yayin da ya ke gabatar da jawabin rufe taron, Ban Ki Moon na mai cewar:

„ Yau lokaci waswasi a game da yaƙi da taɓarɓarewar muhhali ya wuce.

Hukumar majalisar Ɗinkin Dunia mai kulla da al´ammuran cenje-cenjen yanayi ta gudanar da bincike, ta kuma gano cewar, ɗan Adama ke da alhakin taɓarɓarewar muhhali.

Kazalika, ƙurrarun masana sun tabbatar da hakan.

Saƙo na a nan shine, a yanzu mun san idan ciwo ya ke, kenan sai mu nemi magani.

Idan kuma mu ka yi sako –sako, to babu shakka, gurɓacewar yanayi zata hadasa ta´adi mai yawa.“

Wanantaro namatsayin na share fage ga babantaron da zai gudana a watan desember mai zuwa, a ƙasar Indonesia, wanda a sakamakon sa, a ke kyauttata zaton shinfiɗa wata sabuwar taswira kare dunia, daga ɗumamar yanayi.