1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron mai na duniya

September 28, 2005

A taron kasa da kasa a kan mai da ake yi akan mai a ATK an tabbatar da cewar adanin mai dake akwai zai wadatar zuwa 2030

https://p.dw.com/p/BvZM

Hakan zai samu ne bisa sharadin cewar za a zuba kwatankwacin dalar Amurka miliyan dubu 100 a kowace shekara domin sabunta matatun mai da kuma binciko wasu sabbin rijiyoyi, kamar yadda aka ji daga Rex Tillerson, shugaban kamfanin mai na Exxon Mobil a taron kasa da kasa akan man fetur Afurka ta Kudu. Wanda kuma ya ci gaba da cewar:

Muna da cikakkiyar masaniya a game da cewar akwai wadatar mai a duniya. Domin kuwa a wani binciken yanayin kasa da kasar Amurka ta gudanar an gano cewar akwai wata dama ta cimma adanin mai da yawansa ya kai na garewani miliyan dubu har sau dubu biyu. Wannan adadi kuwa shi ne mafi yawa da aka taba hakowa a cikin tarihin dan-Adam a doron kasa. Amma a daya bangaren ana samun karuwar bukatar man fiye da kima, inda aka yi hasashen cewar a cikin shekaru 25 masu zuwa bukatar zata karu daga kashi 70 zuwa kashi 80%, musamman daga bangaren kasashe masu matsakaicin ci gaban masana’antu. Domin cimma biyan bukata wajibi ne a binciko sabbin rijiyoyin da zasu cike wannan gibi, saboda dogaro da za a ci gaba da yi akan man fetur wajen samun makamashi ko da kuwa an fadada ayyukan tashoshin makamashin nukiliya da na zafin haske rana da karfin iska da ragowarsu.

Kasar Saudiyya, wacce ta fi kowace kasa haka da kuma cinikin mai a duniya ta bayyana shirinta na kara yawan abin da take hakowa a rana, wanda a yanzun ya kama garewani miliyan 11, kamar yadda aka ji daga bakin ministan makamashi na kasar Ali Al Naimi:

Manufarmu ita ce mu yi karin garewani miliyan uku akan abin da muka saba hakowa a rana kuma muna kashe makudan kudi wajen kyautata ayyukan hakan man da kuma binciko sabbin rijiyoyi. Nan da shekara ta 2009 zamu samu ikon hakan garewani miliyan 12 da rabi a rana akan hanyarmu ta cimma garewani miliyan 15 a kowace rana ta Allah.

Ministan makamashin na Saudiyya ya kara da bayanin cewar ko da yake kasar ba zata iya biya wa kowa da kowa bukatarsa ba, amma akalla wannan mataki nata zai shawo kan ragowar kasashen dake da dimbim arzikin mai kamarsu Kanada da Irak da Iran su bi saunta. Kazalika akwai kasashen Afurka, wadanda nan ba da dadewa ba za a rika damawa da su sosai da sosai a harkar cinikin mai a duniya sakamakon dimbim arzikin man da Allah Ya fuwace musu. Dukkan kamfanonin mai da kasashen da Alla Ya fuwace musu arzikin man sun hakikance cewar makomarsu ta ta’allaka ne akan wannan ma’adani, kamar yadda bayani ya fito daga bakin ministan makamashi na kasar Venezueler, wanda ya ce mai yiwuwa kafin nan da shekara ta 2030 a cimma karin adanin da ya kai na garewani miliyan dubu har sau dubu uku zuwa dubu bakwai, a saboda haka babu wani dalili na shiga rudu da rashin sanin tabbas.