1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron makomar Jam´iyyar ANC ya shiga rana ta biyu

Ibrahim SaniDecember 17, 2007
https://p.dw.com/p/CcVk

An shiga rana ta biyu aci gaba da taron ƙolin wuni huɗu na Jam´iyyar ANC a Afrika ta Kudu. Bayanai sun ce taron zai kai ga zaɓen sabon shugaban Jam´iyyar da kuma aiwatar da wasu sabbin sauye-sauye. Ana dai wannan takara ne a tsakanin shugaba Thabo Mbeki da kuma tsohon mataimakinsa Mr Jacob Zuma. Takarar shugabannin biyu a yanzu haka ta haifar da darewar Jam´iyyar izuwa gida biyu. A yayin da yake jawabi gaban taron, Mr Mbeki ya ɓukaci haɗin kan ´ya´yan Jam´iyyar, don cimma burin da aka sa a gaba. Mr Mbeki dake neman tazarce a karo na uku a wannan muƙami na fuskantar ƙalubale daga tsohon mataimakinsa, Mr Jacob Zuma. Duk da zarge-zargen cin hanci da rashawa daya dabaibaye Mr Zuma, rahotanni sun ce Zuma ka iya lashe wannan zaɓe. Hakan dai nada nasaba ne da karɓuwarsa, a tsakanin talakawa da kuma ma su fada aji a Jam´iyyar ta ANC.