1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron manyan kasashe a Berlin kan Iran

Zainab A MohammadMarch 30, 2006
https://p.dw.com/p/Bu76

Manyan kasashen duniya sun bukaci Iran data darajawa kaidojin MDD na dakatar da shirin Nucleanta,idan kuwa ba haka ba zaa mayar da ita saniyar ware,amma hakan bai razana Iran din ba.Britania tace babu shakka zata fuskanci takunkumi daga mdd ,idan har taki dakatar da sarrafa sinadran uranium,wanda ake gani zata iya kera makamai dasu.Iran wadda ta hakikance cewa tana kokarin samarda makamashi ne na nuclear amma ba makamai ba,tayi watsi da zartarwar komitin sulhu a jiya laraba,adangane da waadin kwanaki 30.Akan hakane ministan harkokin wajen jamus Frank-Walter Steinmeir yace zabi ya ragewa Iran nacigaba da sarrafa sinadaran uranium,wanda zai mayar da ita saniyar ware ,ko kuma ta koma teburin sulhu.

Itama sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice ,daya daga cikin mahalarta taron kamata yayi ace iran tayi maraba da wannan yunkuri na su akokarin warware rikicin ta na nuclear,musamman kasancewar baki ya zo daya.