1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron manyan kasashe uku na kungiyyar Eu akan Iran

Ibrahim SaniJanuary 12, 2006

Takaddamar nukiliyar kasar Iran da kasashen yamma na neman daukar sabon salo, bayan matakin baya bayan nan da Iran ta dauka

https://p.dw.com/p/Bu2T
Hoto: dpa

Ya zuwa yanzu dai a cewar rahotanni babbar barazana da wannan mataki na Iran keyiwa kasashen yamman, ba zai wuce tunanin cewa kasar ta Iran na kokarin kera makamin nukiliya bane, wanda tuni a can baya mahukuntan na Iran suka karyata wannan batu da cewa bashi da tushe balle makama.

Da alama dai irin wannan tunani shiya haifar da taron kolin ministocin harkokin wajen kasashen

Kungiyyar Eu uku, wato na Jamus da Faransa da Biritaniya da kuma babban jami´in dake kula da matakan ketare na kungiyyar, wato Javier Solana, a nan birnin Berlin na nan tarayyar Jamus.

Jim kadan da kammala wannan taro nasu, ministan harkokin wajen Jamus, Frank Walter Steinmeier ya

tabbatar da cewa wannan al´amari abu ne daya zo musu makura,dake bukatar maganin gaggawa.

Mr Frank Walter Steinmeir ya fadi hakan ne kuwa a lokacin taron manema labarai daya gudanar tare da takwarorin sa daga Faransa da Biritaniya a hannu daya kuma da Javier Solana, jim kadan da kammala taron kolin na su.

Shi kuwa Jack Straw,ministan harkokin wajen Biritaniya, cewa yayi wannan mataki da kasar ta Iran ta dauka abu ne daya kaucewa tsari.

A gaba daya dai,taron kolin na wuni daya ya tabbatar da cewa lokaci yayi daya kamata a shigo da Mdd cikin wannan harka don tursasawa kasar ta Iran martaba dokokin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya da Mohd El baradei kewa jagoran ci.

Bugu da kari,taron ya kuma bukaci hukumar kula da makamashin nukiliyar ta duniya, data kirawo taron jami´an zartarwar ta don tattauna wannan batu,don daukar matakin daya dace akan kasar ta Iran.

Shi kuwa jami´in dake kula da matakan ketare na kungiyyar ta Eu, wato Javier Solana cewa yayi,duk da wannan kiki ka kann da ake ciki,kofar tattaunawar diplomasiyya don warware wannan takaddama a tsakanin kungiyyar da kasar ta Iran a bude take.

Bayanai dai sun nunar da cewa manyan kasashe uku na kungiyyar ta Eu da alama nada ra´ayi ne irin na mahukuntan Amurka akan kasar ta Iran, na cewa kasar na kokarin kera makamin Aton a boye da sunan nukiliya ce ta bunkasa hasken wutar lantarki a kasar.

Rahotanni dai sun nunar da cewa,bayan wani bayani mai sosa rai daya gabatar a game da nukiliyar kasar ta Iran a kwana biyu da suka gabata,tsohon shugaban kasar ta Iran Hashimi Rafsanjani a dazu da rana ya tabbatar da cewa kace nace dake ci gaba da wanzuwa a game da wannan aniya ta Iran,ya kai kokoluwa, a don haka kasar zata ci gaba da aiwatar da matakin data dauka.

Idan dai za a iya tunawa a jiya laraba, Shugaban kasar wato Mahmud Ahmadinajed ya tabbatar da cewa babu gudu babu ja da baya game da ci gaba da aiwatar da wannan mataki duk kuwa da bazrazanar da akewa kasar na ladaftar da ita a gaban kwamitin sulhu na Mdd.

A waje daya ma dai kasar Russia, dake hulda ta kusa da kasar ta Iran,musanmamma akan batun makamashi, bayyana damuwar ta tayi a game da wannan mataki na Iran.

Kafafen yada labaru sun rawaito ministan harkokin wajen kasar, wato Sergei Lavrov na fadin cewa a cikin farko farkon mako mai kamawa, wakilan kasashen Jamus da Biritaniya da Faransa da Russia da kuma kasar sin zasu gudanar da wani taro a birnin London don tattauna wannan batu, bisa manufar daukar matakin daya dace.

Daga dai cikin jerin wadannan kasashe, kasar Jamus ce kawai bata daga cikin mambobin dake da zaunanniyar kujera a kwamitin sulhu na Mdd. Ya zuwa yanzu dai babu tabbacin ko wannan taron zai bukaci kasancewar kasar ta Iran a cikin sa ko kuma a´a. .