1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron manyan kasashen duniya a game da Iran

January 16, 2006
https://p.dw.com/p/BvC0

Kasashe biyar dake da zaunanniyar kujera a kwamitin sulhu na Mdd da kuma Jamus na gudanar da wani taron koli a birnin London don cimma matsaya guda akan matakin da kasar Iran ta Dauka.

Kasashen da suka hada da Amurka da Biritaniya da Faransa da Russia da kasar sin a hannu daya kuma da Jamus na gudanar da taron ne don duba yiwuwar daukar matakin kakabawa kasar ta Iran takunkumi.

Ire iren wadannan tarurruka sun samo asaline bayan da mahukuntan na Iran suka bayar da sanarwar ci gaba da bincike a wasu tashohin nukiliyar su dake cikin kasar.

Ya zuwa yanzu yanzu dai kasashen yamman tare da Amurka sun zargi kasar ta Iran da kokarin kera makamin nukiliya, wanda kuma tuni kasar ta Iran ta karya hakan da cewa nukiliyar da take kokarin kerawa na bunkasa hasken wutar lantarki ne, amma bana tashin hankali ba.