1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron masu bada gudumowa na Aids da fuka a Berlin

September 27, 2007
https://p.dw.com/p/BuA8

A birnin Berlin masu bada gudumowa ga asusun kasa da kasa na yaki da cutar Aids da tarin fuka da Malaria suna halartar wani baban taro na kwana guda tare da nufin tara euro biliyan 6 nan zuwa 2010.Wajn jawabinta na bude taron shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a matsayinta na shugaba mai ci yanzu ta kasasahe 8 masu arzikin masaantu tayi kira da inganta shiryukan kula da lafiya .Tace ya kamata a hade harkokin asusun da kuma aiyukan cibiyoyin hukumar lafiya ta duniya da babban bankin duniya wajen yaki da wadannan cututtuka wanda tace talauci ke kara yaduwarsu.Tsohon sakataren MDD Kofi Annan a nashi bangare yace ana samun tsaiko ga tabbatar da a cimma burin rage cututuukan da rabi nan zuwa 2015 musamman wajen magancesu.Ya zuwa yanzu dai asusun ya samarda taimako ga masu cutar Aids su miliyan daya da dubu dari daya,da kuma masu tarin fuka miliyan uku da dubu dari uku yayinda kuma ya samarda miliyoyin gidajen sauro masu maganin kashe sauro.