1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Ministocin Gamayyar Turai a Brussels

September 11, 2010

Ministocin Turai na cigaba da mahawara kan yiwuwar shigar Turkiyya Kungiyar

https://p.dw.com/p/P9xE
Guido WesterwelleHoto: AP

Ministocin harkokin wajen ƙasashe EU  sun shiga rana ta biyu na taronsu a birnin Brussels inda suke tattauna batutuwa da dama. Babban Agendar taron dai  mawahara dangane da da cewa ko akasin haka na shigar Turkiya cikin wannan ƙungiya. Tun a shekara ta 2005 ne Turkiya ke neman kujera a ƙungiyar ta gamayyar Turai. Amma kuma kasashe Faransa da kuma Jamus na ci gaba da nuna adawarsu da duk wani yunƙuri na bai wa ankara gurbi a cikin kungiyar ta EU. Ministan harkokin wajen Jamus  Guido westerwelle ya ce ya na da mahimmaci ƙasashe na Eu su ci gaba da ɗasawa da Turkiya.

 Ya ce "ba wai kawai saboda ta fannin tattalin arziki ba. Ina ganin yana da matukar muhimmanci a ɓangaren Turai, ta darajawa Turkiyya, tare da la'akari da yadda za'a gudanar da huldoɗi da ita, saboda gudunmawar da ta ke badawa a fannoni daban daban ciki kuwa har da neman wanzar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya".

 Taron ministocin harkokin wajen Turan yazo ne a daidai lokacin da 'yan Turkiyyan ke  shirin kaɗa kuri'ar raba gardama gobe, a dangane da gyaran kundun tsarin mulkin ƙasar, domin yin daidai da kudurorin ƙungiyar ta EU.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar

Edita:           Abdullahi Tanko Bala