Taron ministocin harakokin tsaro na ƙasashen EU.
March 7, 2006Ministocin harakokin tsaro na ƙasashe membobin ƙungiyar gamayya turai, sun yi zamman taro yau, a birnin Innsbruck, na ƙasar Austriya.
Mahimman batutuwan da ke ajendar wannan taro, sun haɗa da aika dakarun shiga tsakani a Jamhuriya Demokraɗiyar Kongo, da batun girka assusun talafawa bincike, a kan harakokin tsaro a nahiyar turai.
Kazalika mahalarta taron, sun yi masanyar ra´ayoyi, a game da al´amuran ta´adanci a dunia.
A ƙarshen watan desember da ya wuce, Majalisar Ɗinkin Dunia, ta buƙaci ƙungiyar gamayya turai, ta aika dakarun shiga tsakani, a Jamhuriya Demokraɗiya Kongo da ke fama da rikicin tawaye.
A tsarin da su ka shirya, ƙasashen EU za su tura bataliya guda da za ta ƙunshi sdakaru dabu 1 zuwa 1250, a wannan yanki na tsakiyar Afrika.
Saidai ,a sakamakon mahaurorin da su ka gudanar yau, a a kan wannan batu, ministocin tsaron EU, ba su cimma matsaya ba, ta bai ɗaya, a game da aika wannan runduna, amma za su ci gaba da tuntubar juna, kamar yadda ministan harakokin tsaron Jamus, Franz Josef Jung ya bayyana.