1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin harakokin waje a birnin Berlin

March 30, 2006
https://p.dw.com/p/Bv3h
Hoto: AP

Yau ne a birnin Berlin na an Jamus ministocin harakokin waje, na ƙasashe masu kujerun dindindin a komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia, da kuma ministan harakokin wajen Jamus, Frank walter Steinmeir za su buɗa zaman taro, a game da rikicin makaman nukleyar ƙasar Iran.

Wannan taro da zai samu halartar sakataran harakokin wajen ƙungiyar gamayya turai, na ɗauke da burin kussanto ra´ayoyin ƙasashe masu faɗa aji a dunia kan wannan batu mai sarƙƙaƙiya.

Bayan sati 3,na mahaurori, jiya ne komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia, ya samu cimma nasarar gabatar da mataki na bai ɗaya, wanda a sakamakon sa, ya baiwa Iran wa´adin wata ɗaya, na ta daina ayyukan saraffa makaman nuklea.

Komitin ya bukaci shugaban hukumar yaƙi da yaɗuwar makaman nuklea, Mohamed El Bardadei, ya gabatar da rahoto, a ƙarshen watan ɗaya, domin tantance, I ko a´a hukumomin Iran, sun bi umurnin Majalisar Ɗinkin Dunia.

An cimma wannan mataki, bayan an yi ta kai ruwa rana, tsakanin ƙasashen China da Rasha, masu nuna goyan bayan ga Iran, da kuma Amurika da turai, a hannu ɗaya dake buƙatar gurfanar da ita, gaban komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia.