1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin harakokin wajen ƙasashen larabawa a birnin Aƙahira

April 12, 2006
https://p.dw.com/p/Bv29

Yau ne a birnin Alƙahira, na kasar Masar, ministocin harakokin wajen ƙasashen larabawa, su ka buda zaman taro, domin tantanawa a game da rikicin ƙasar Iraki.

To saidai, wanda abin ya shafa, wato Irakiyawa, bas u halarci taron ba.

Gwamnatin Iraki, ta ɗauki wannan mataki, domin maida martani, ga kalamomin shugaban ƙasar Masar, Osni Mubarak, inda ya ambata cewar, yan shia´ar Iraki, yan amshin shatar Iran ne.

Babban burin da ake bukatar cimma, a wannan zaman taro, shine samar da hanyoyin warware rikicin da ya ƙi ya ƙi cenyewa Irak.

Ministocin za su hiddo sanarwar ƙarshen taro, wace, zata kira ga ɓangarori, masu yaƙar juna, da su tsaigaita wuta, sannan yan siyasa su cimma daidaiton girka gwamnati.

To saidai, masharahanta na ɗaukar wannan taro, tamkar ihunka banza,kasancewar bai samu goyan baya ba, daga gwamnatin Iraki.