1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin harkokin waje na EU a Sydney

September 7, 2007
https://p.dw.com/p/BuCA

Ministocin harkokin waje na kungiyar tarayyar turai sanar da manufarsu na cimma matsaya guda adangane da garon bawul wa kungiyar cikin watan gobe,duk da zaben kasar Poland dake barazana,da matsin lamba da kasar Britania ke fuskanta adangane da kuriar raba gardama tsakanin alummomin kasar kann wannan batu.Adangane da yancin kada kuriu musamman a bangaren sabbin wakilan kasashe kuwa,poland tace tana da raayi guda da Britania,ata bakin ministar harkokin wajen kasar Anna Fotyga….

„Tace Tace an cimma wannan matsaya dangane da yancin kada kuriu ne a lokacin taron kasashen turai ,amma dole ne mubi sannu a hankali wajen tantance bnatum“

A watan yunin daya gabata nedai shugabannin Eu suka cimma kwaryakwaryar yarjejeniya na yiwa kundun tsarin mulkin kungiyar garon bawul,domin maye gurbin wadda kasashen faransa da Holland sukayi watsi da ita a 2005.