1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

TARON MINISTOCIN HARKOKIN WAJE NA KUNGIYAR EU DA KASASHEN YANKIN BAHAR RUM A BIRNIN DUBLIN.

YAHAYA AHMEDMay 6, 2004

Kwana daya bayan taron da aka yi a birnin New York, don tattauna batun farfado da shawarwarin zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya ne, ministocin harkokin wajen kasashen Kungiyarr Hadin Kan Turai, suka yi wani taro da takwarorinsu na kasashen yankin Bahar Rum da wakilan Hukumar Mulkin Kan Falasdinawa, a birnin Dublin. Wannan taron dai, na daya daga cikin taruka kalilan, inda wakilan Isra’ila da na kasashen Larabawa ke zama a kan teburin shawarwari daya.

https://p.dw.com/p/Bvjs
Ministan harkokin wajen Masar, Ahmed Maher, da tawagarsa, yayin da suka isa a gun taron na Dublin.
Ministan harkokin wajen Masar, Ahmed Maher, da tawagarsa, yayin da suka isa a gun taron na Dublin.Hoto: AP

A gun taron na Dublin, maneman labarai sun yi wa jami’in Hukumar Falasdinu mai kula da harkokin waje, Nabil Schaat, tambaya, inda suka nemi su san ko mene ne dalilin da ya sa bai gana da ministan harkokin wajen Isra’ila, Silvan Shalom ba. Nabil Schaat dai, bai ce musu uffan ba, wucewarsa kawai ya yi, ya shiga zauren taron.

A zahiri dai, ba a shirya ganawar jami’an biyu a gun taron ba. Jami’in na Hukumar Falasdinawa, Nabil Schaat dai, ya nuna gamsuwarsa da bayanan da masu shiga tsakani a rikicin Gabas Ta Tsakiya, wato Amirka, da Kungiyar Hadin Kan Turai, da Rasha da kuma Majalisar Dinkin Duniya suka yi. Ya kuma bayyana cewa, janyewar Isra’ila daga zirin Gaza ba za ta sami wata ma’ana ba, sai an jibinta ta da daftarin samad da zaman lafiyar nan da masu shiga tsakanin suka tsara suka kuma amince da shi.

"Idan Isra’ila ta janye da gaske daga zirin Gazan, za mu yi murrna. Amma, a nan al’amura daban suke. Sai da Isra’ilan ta sake duk sharudda dangane da janyewar kafin ta tura wakilanta zuwa Washington.. Ta dai dage kan cewar, ba za ta yarda mu gina filin jirgin sama ba, ko tashar jirgin ruwa, ko kuma samun damar yin sabbin gine-gine a can inda za ta janyen ba. Duk da hakan dai, `yan jam’iyyar Likud din sun yi watsi da shirin. A nawa ganin dai, shirin na Firamiya Sharon, ba zai sami karbuwa a ko’ina ba. A yanzu dai, daftarin samad da zaman lafiyar ne kawai, taswirar da za ta iya kai mu ga cim ma zaman lafiya mi dorewa."

Wakilin na Falasdinawa dai yana matashiya ne da shirin da Firamiyan Isra’ila Ariel Sharon ya gabatar wa `yan jam’iyyarsa, don su amince da shi, kafin ya ba da umarnin janyewa daga zirin Gazan. Amma a kuri’un da suka ka da a ran lahadin da ta wuce, sun yi watsi da shirin gaba daya.

Ministan harkokin wajen Jamus, Joschka Fischer, a cikin wata fira da ya yi da gidan rediyon Deutsche Welle, ya bayyana cewa, lokaci ya zo da ya kamata, a yi cikakken nazari, kan yadda al’amura ke wakana yanzu a Gabas Ta Tsakiyan. Ya dai yi marhabin da sanarwar da rukunin masu shiga tsakani cikin wannan lamarin ya bayar a birnin New York:

"Rukunin, ya yarje kan wani batu mai muhimmanci. Kamata kuma ya yi, a yi nazarin mai zurfi kan yarjejeniyar. Sabili da haka ne dai muka kira wannan taron, don mu ji daga bakin wadanda abin ya shafa, mu kuma dubi yadda za mu gudanad da nazarin, ko kuma ba da wasu sabbin shawarwari."

A taron na yau dai, ministocin harkokin wajen Kungiyar Hadin Kan Turan, za su yi shawarwari daban-daban ne, da wakilan kasashen Larabawan da kuma na Isra’ila, don gano yadda za a sake farfado da shawarwarin zaman lafiyar a Gabas Ta Tsakiya.

A makwanni uku da suka wuce dai, a wani taron da suka yi a kasar Irealand, ministocin kungiyar EU din, sun yi kakkausar suka ga yin amfani da karfin soji da Isra’ilan ke yi a yankunan Falasdinawa. Sun kuma nuna rashin jituwarsu da tafiyar hawainiyar da Hukumar Falasdinawan ke yi a kan batun samad da zaman lafiyar.