1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Außenminister EU

February 22, 2010

Dambarwa kan Fasfo din Jabu na kasashen Turai

https://p.dw.com/p/M85A
Wasu Ministocin harkokin wajen tarayyar Turai a lokacin taronsu a BrusselsHoto: picture-alliance/dpa

►Ministocin harkokin waje na ƙasashen ƙungiyar tarayyar Turai sun baiyana matukar damuwarsu dangane da amfani da Fasfunan Jabu na wasu ƙasashen Turan wanda aka zargin Jamián leken asirin Israila "Mossad" da aikatawa don aiwatar da kisan jamiín Hamas a Dubai.

Ministocin harkokin wajen sun hallara ne a Brussel domin taron da suka saba gudanarwa a kowane wata. Ana sa ran Ministocin zasu nemi jin bahasi game da kisan gillar da aka yiwa wani Jamiín Hamas a Dubai. Ko da yake wannan baya cikin jadawalin taron amma ministocin na tarayyar Turai na buƙatar samun cikakken bayanai kan yadda aka yi amfani da Fasfunan jabu na wasu ƙasashen turai wajen aikata wannan ɗanyen aikin. Ana dai zargi hukumar leƙen asirin Irsraila Mossad da aikata kisan inda suka yi amfani da fasfunan ƙasashe daban daban na turai domin ɓadda kama.

Batutuwan muhawara dake cikin Ajandar taron Ministocin harkokin wajen an EU sune dai waɗanda aka saba, wato batun Nukiliyar Iran da Afghanistan da Zimbabwe da halin da ake ciki a Haiti da Ukrain da kuma Belarus.

Ministocin harkokin wajen zasu kuma mayar da hankali kan wani batun duk da cewa baya da alaƙa da taron nasu. Wannan batu dai shine ziyarar Ministan harkokin wajen Israila Avigdor Lieberman zuwa Brussels. An jima dai da shirya wannan ziyara, sai dai kuma a yanzu ta sami jan hankali sosai. Wasu daga cikin Ministocin na son ganin Ministan harkokin wajen Israilan Avigdor Lieberman domin yi masa tsauraran tambayoyi. Tambayar kuwa ta danganci kisan Mahmoud al-Mabhuh babban jamií wanda kuma aka yi zargin cewa a tsakiyar watan Janairu da ya gabata ya yiwa ƙungiyar Falasɗinawa ta Hamas safarar makamai daga Dubai.

Avigdor Lieberman
Ministan harkokin wajen Israila Avigdor LiebermanHoto: AP

Abu mafi ɗaukar hankali shine sarƙaƙiyar dake tattare da yanayin da aka yi masa kisan gilla wanda aka ɗora alhakinsa akan hukumar leƙen asirin Israila Mossad. Babban sufeton yan sanda Dubai yace yayi imanin jamián na Israila ne suka aikata kisan. Wasu Jakadun yammacin turai ma dai basu fidda tsammanin hakan ba, hasali ma wata Jaridar Birtaniya da aka wallafa a ƙarshen mako ta ruwaito cewa Firaministan Israila Benjamin Netanyahu shi da kansa ne ya bada umarnin aiwatar da kisan.

Britischer Biometrie-Paß
Fasfo ɗin ƙasar BirtaniyaHoto: AP

Dambarwar da ta kunno kai dai a yanzu tsakanin Israila da gwamnatocin ƙasashen turai, ita ce tawagar mutane goma sha ɗaya da suka tsara aiwatar da kisan sun yi amfani ne da Fasfunan Jabu na ƙasashen turai musamman Ireland da Birtaniya da Faransa da kuma Jamus. An gano cewa Fasfo ɗin na Jamus wanda ya sha shige da fice an bayar da shi ne a Cologne. A yanzu dai jamií mai gabatar da ƙara ya buɗe binciken domin gano ko daya daga cikin mutanen da ake zargi da kisan sun aikata magudi wajen sauya bayanai a jikin fasfo ɗin.

Babban abin takaicin shine a kasar Ireland yadda mutanen suka sami Fasfuna ɗaiɗai har guda biyar na hukuma. Ministan harkokin wajen na Ireland ya nemi ganawa da Lierberman domin baiyana masa ɓacin ransu  tare kuma da neman a baiyana masa dalilan aikata wannan mummunan laifi.

Israilan dai ta ƙi cewa komai game da abinda jamián hukumar leken asirin ta Mossad suka aikata. Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle tuni ya bukaci bincike da kuma bada cikakken bayanai gamae lamarin.

Mawallfa: Bohne, Martin/Abdullahi Tanko Bala Edita Yahouza Sadissou Madobi