1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin harkokin wajen KTT akan Palasdinu

June 18, 2007

Ministocin harkokin wajen KTT na taro a Luxemburg domin nazarin martanin da zasu mayar akan halin da ake ciki a Palasdinu.

https://p.dw.com/p/BtvK

Ita dai KTT bata yi wata rufa-rufa ba wajen bayyana cikakken goyan bayanta ga shugaba Mahmud Abbas da kungiyarsa ta Fatah, wadda a halin yanzu haka take da ikon yankin yammacin gabar kogin Jordan. Kafin dai a shiga taron na Luxemburg ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier yayi nuni da cewar:

“A ‘yan tsurarun kwanakin da suka wuce dai mun ga yadda al’amura ke dada yin tsamari da tashe-tashen hankula ba kakkaunatawa, kuma dakarun kungiyar Hamas ne ke da alhakin lamarin.”

A yanzun dai wajibi ne a yi bakin kokari wajen goya wa sabon P/M Salam Fahhad baya in ji kantoman KTT akan manufofin ketare Javier Solana. Ana dai batu a game da sassauta takunkumin dora hannu akan kudaden taimakon da aka aza wa Palasdinawa, ko da yake har yanzu ba a tsayar da wata shawara akai ba. Amma Solana ya ce za a taimaka wa mahukuntan Palasdinawa a yankin yammacin gabar kogin Jordan da wasu ‘yan kudi.

“Za a yi gabatar da wani bangare na kudin kai tsaye. Dangane da Zirin Gaza kuwa sai an sake bitar lamarin sosai. A sakamakon haka ya zama wajibi mu ci gaba da tattaunawa da P/M Fajad. Tun a jiya da dare muka fara tuntubarsa, amma ya nuna cewar a dai halin da ake ciki yanzun bai san yadda zai billo wa maganar ba. Sai dai kuma tilas ne ya gabatar da wani kasafin kudi, wanda zai ba shi damar taimaka wa mutane a yankin yammacin gabar kogin Jordan da zirin Gaza.”

Ministocin harkokin wajen na kasashen KTT zasu yi musayar yawu da ministar harkokin wajen Isra’ila Tzipi Livni a game da matakai na hadin guiwa da zasu iya dauka domin rufa wa shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas baya tare da sabuwar gwamnatin da ya nada. Isra’ila ta dora hannu kan kudaden kwasta da haraji na Palasdinawa, wadanda yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 600. Solana ya ce wajibi ne Isra’ila ta danka wa sabuwar gwamnatin Palasdinu wadannan kudade, saboda hakan zai taimaka wa al’umar Palasdinu matuka ainun. Ma’amalla da sabuwar gwamnatin kuwa ta danganta ne da amincewarta da hakkin wanzuwar Isra’ila, lamarin da a yanzun ba zai ta’azzara ba tun da an kakkabe kungiyar Hamas daga mulki. Amma kuma a daya bangaren ita Hams ce ke da rinjaye a majalisar dokoki, wadda shugaba Mahmud Abbas ke bukatar goyan bayanta domin tabbatar da sabuwar gwamnatinsa akan kujera a cikin kwanaki talatin masu zuwa.