1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Ministocin Harkokin Wajen KTT

December 13, 2005

A jiya litinin ministocin harkokin wajen KTT suka gudanar da taronsu a Brussels

https://p.dw.com/p/Bu3R
Taron ministocin harkokin wajen KTT
Taron ministocin harkokin wajen KTTHoto: AP

A dai halin da ake ciki yanzu Jamus ta kuduri niyyar gabatar da wata takardar kudurin dake Allah waddai da kasar Iran a hukumance a zauren taron kolin shuagabannin kasashen kungiyar ta tarayyar Turai a karshen wannan makon. An saurara daga bakin wani kakakin gwamnati a fadar mulki ta Berlin yana mai fadin cewar wadannan kalamai na cin mutuncin Isra’ila da suka fito daga bakin shugaba Mahmud Ahmadinajad na kasar Iran, kalamai ne na Allah waddai wadanda ba za a amince da su ba. A nasa bangaren ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya fada a zauren taron na Brussels cewar a sakamakon wadannan lafuzza daga bakin shugaban kasar Iran a yanzu al’amura zasu dada yin tsamari a game da sabanin da ake yi akan shirin kasar na tashar makamashin nukiliya. Ministocin harkokin wajen na kasashen KTT, a zauren taron nasu a Brussels, sun yi kira ga Iran da ta dauki nagartattun matakai na kare hakkin dan-Adam, domin kuwa bana al’amura sun dada rincabewa dangane da kiyaye hakkin dan-Adam a kasar ta Iran duk da kiraye-kirayen da aka sha yi game da haka. Ita dai KTT a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da Iran akan shirinta na makamashin nukiliya, amma fa idan ita Iran a nata bangaren ta ki ta tabuka wani abin a zo a gani, to kungiyar zata ba da goyan baya ga manufar kai maganar gaban kwamitin sulhu na MDD domin zatar da wani kuduri akanta. Amurka da kasashen KTT na zargin Iran ne da kokarin kera makaman kare dangi kuma a sakamakon haka aka dakatar da shawarwarin da ake yi da ita. Ita ma majalisar Turai dake Straßburg ta la’anci kiran da shugaban Iran yayi na cewar a maido da Isra’ila zuwa Jamus ko Austriya saboda wai ta haka ne za a shawo kann rikicin Yankin Gabas ta Tsakiya. Daya matsalar da ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar ta tarayyar turai ta duba kuma ita ce maganar kasar Macedoniya, inda suka kasa cimma daidaituwa akan amincewa da ita a matsayin daya daga cikin kasashen dake fafutukar a karbesu a kungiyar, kuma a sakamakon haka za a gabatar da maganar a zauren taron kolin shuagabannin kasashenta a karshen mako, kamar yadda sakataren harkokin wajen Birtaniya Jack Straw. Kasashen Faransa da Netherlands ne suka yi dari-dari da wannan batu ta la’akari da sabanin da ake fama da shi akan daftarin tsarin mulki bai daya tsakanin kasashen kungiyar ta tarayyar Turai. Ministan harkokin wajen Faransa Philippe Douste-Blazy ya ce za a iya sake waiwayar kasar ta Macedoniya ne bayan an samu haske a game da makomar kafofin kungiyar shekara mai zuwa. A zauren taron nasu a jiya litinin ba su tabo maganar kasafin kudi na dogon lokaci da aka dade ana sabani kansa ba, wanda kuma ke taka muhimmiyar rawa a game da karbar karin kasashe a kungiyar. A gobe laraba P/M Birtaniya Tony Blair zai gabatar da wata shawara, bayan da aka yi mata gyaran fuska, kafin a shiga taron kolin shuagabannin daga ranar alhamis idan Allah Ya kai mu.