1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

taron ministocin harkokin wajen tarayyar Turai a Luxemburg

October 18, 2005
https://p.dw.com/p/BvOr

Ministocin harkokin wajen kasashen KTT sun yi kira da a karfafa ba da hadin kai tsakanin kasa da kasa don daukar matakan rigakafin yaduwar murar tsuntsaye. Wata sanarwa da suka bayar a karshen wani taro na musamman da suka yi a Luxemburg ministocin sun ce cutar na barazana ga duniya baki daya. Bayan bullar nau´in cutar mai hadari ga dan Adam a kasashen Turkiya da Romaniya, kungiyar EU mai hedkwata a birnin Brussels ta sanya takunkumin shigowa da kaji da sauran dabbobi masu fikafikai daga kasashen biyu. A jiya litinin kuma an tabbatar da bullar cutar a Girika, wato karon farko da cutar ta bulla a wata kasa membar kungiyar EU. To sai dai har yanzu ba´a fayyace ba ko cutar mai hadari ce ga dan Adam.