1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

241108 Ministerrat Deutschland Frankreich

Mohammad AwalNovember 25, 2008

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel a ranar Litinin ta gana da shugaban Faransa, Nicholas Sarkozy a Paris.

https://p.dw.com/p/G1d1
Sarkozy da MerkelHoto: AP

Taron ƙolin da ƙasashen biyu suka saba yi ko wane wata shidda, a wannan karo ya maida hankali ne kan rikicin kasuwannin hada-hadar kuɗi da ake fama da shi yanzu.

Jamus da Faransa gaba ɗaya sun nuna cewar ba zasu rage harajin da aka saba ɗorawa cinikin kayaiyakin yau da kullum ba tare da fatan yin haka zai ƙara yawan kuɗaɗe a aljihun jama'a. Shugabar gwamnati, Angela Merkel ta ce ƙasashen biyu sun daidaita game da hakan a lokacin taron ƙolin nasu.

Wataƙila rage haraji a kan kayan masarufi na yau da kullum yana iya zama mai amfani ga wasu ƙasashe, amma ba haka abin yake ba ga Jamus da Faransa. Mun daidaita matuƙa tsakanin mu a game da wannan ra'ayi.

Pirayim ministan Ingila, Gordon Brown a farkon wannan mako ya sanar da cewar zai rage haraji kan kayan buƙatun yau da kullum, to amma shugabar gwamnatin Jamus, Merkel ta ce ya zuwa yanzu ba ta ga amfanin ɗaukar irin wannan mataki ba. A maimakon haka, wajibi ne tare da taimakon ƙungiyar haɗin kan Turai a Bruessels, a taimakawa fannoni dabam dabam na tattalin arzikin nahiyar Turai. Ta ce Jamus ta gabatar da irin wannan tsari na taimako, da tuni ma aka yi nazarin sa a majalisar dokoki, alal misali, ta hanyar ɗauke harajin hukuma kan sabbin motoci da kuma rage haraji ga masu sana'oin hannu.

Shugabar gwamnatin ta nunar lokacin ganawar ta a Paris da shugaban na Faransa cewar Jamus ba ta buƙatar shigar da wani ƙarin kuɗi domin aiwatar da shirin ƙungiyar haɗin kan Turai na farfaɗo da tattalin arzikin nahiyar, a sakamakon rikicin da ake ciki yanzu. Duk da haka, Nicholas Sarkozy shugaban Faransa ya nunar da cewar:

Mun daidaita kan cewar wajibi ne a ɗauki ƙarin matakai. Faransa ta fara ɗaukar irin waɗannan matakai da ake buƙata, Jamus har yanzu tana nazari tukuna.

A Faransa dai ana ɗaukar Angela Merkel a matsayin wadda ba ta buƙatar al'amura su ci gaba ne cikin hamzari. Farasawan har yanzu ba su manta da gaskiyar cewar Jamus ta taɓa baiyana adawar ta da wani shiri da aka gabatar na ceto bankuna da kasuwnanin hada-hadar kuɗi a Turai ba, yayin da Merkel ɗin har yanzu take adawa da ƙoƙarin da Nicholas Sarkozy yake yi na ƙirƙiro abin da ya kira gwamnatin da zata kula da tattalin arziki ta ƙasashen dake amfani da kuɗin bai-ɗaya na Euro.

A game da muhimmin al'amari na biyu da aka duba a lokacin taron ƙolin na Faransa da Jamus, har yanzu dai babu wani ƙudiri da aka yanke. Ko da shi ke ƙasashen biyu sun daidaita a game da sharuɗɗan da za'a shimfiɗawa masana'antun ƙera motoci game da yawan hayaƙin da sabbin motoci zasu riƙa fitarwa dake gurɓata yanayin sararin samaniya, to amma kamar yadda Sarkozy ya nunar, cikakken bayani game da hakan sai a lokacin taron ƙolin ƙungiyar haɗin kan Turai ne a tsakiyar watan Disamba za'a gabatar da shi. Shugaban gwamnatin Jamus ta ce:

Amma yana da muhimmanci mu ga cewar wannan mataki na kare yanayin sararin samaniya bai zama sanadin asarar wuraren aikin yi ba, amma wajibi ne mu sami wata hanya da zata daidaita batun kare muhalli da bunƙasar tattalin arziki. A ra'ayi na game da hakan mun gudanar da tattaunawa mai ma'ana kuma ina da ƙarfin zuciyar zamu sami nasarar cimma burin mu.

Angela Merkel shugaban gwamnati ce dake iya baiyana ra'ayin ta kan duk abin da take ganin bai dace ba. Wannan matsayi kuwa bai canza ba ko a bayan taron kolin na fadar mulkin Faransa ta Elysee a Paris ranar Litinin.