1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin kasashen kungiyar ´yan ba ruwan mu

Mohammad Nasiru AwalAugust 17, 2004
https://p.dw.com/p/BvhF
Josip Brotz Tito tsohon shugaban kasar Yugoslabiya
Josip Brotz Tito tsohon shugaban kasar YugoslabiyaHoto: AP

Wasu ababa biyu da aka samu bayan yakin duniya na 2 sune yakin cacar baka da kuma kungiyar kasashen ´yan baruwanmu. Wannan kungiyar ta samo asali ne sakamakon yaki da mulkin mallaka da nuna wariyar launin fata sai kuma bukatar girmama usular MDD. A cikin shekarar 1955 bisa shawarar FM Indiya Jawaharlal Nehru shugabannin Asiya da na Afirka kimanin 24 sun hallara a birnin Bandung dake a tsabirin Java na kasar Indonesia. Wannan taron dai ya kasance wani babban taron kasashen Afirka da Asiya, inda mai saukar baki shugaba Sukarno da shugaban Masar Jamal Abdel Nasser suka taka muhimmiyar rawa. Shi ma shugaban kasar Yugoslabiya na wancan zamani Josip Brotz Tito, wanda yayi gwagwarmayar samar da wata kungiyar kasashen duniya ta daban da zata ba da tata gudummawa a harkokin siyasar duniya, ya nuna goyon baya ga kafa kungiyar kasashe ´yan baruwanmu. A tarurrukan da aka yi na farko a Yugoslabiya a shekarar 1956 da na biyu a birnin Alkahira a shekarar 1961, an yi shirye-shiryen gudanar da taron farko na kungiyar kasashen ´yan baruwanmu, wanda aka yi a birnin Belgrade a watan satumban 1961. A dangane da tserereniyar kera makaman nukiliya tsakanin tsofaffin manyan daulolin duniya wato Amirka, TS, Britaniya, Faransa da kuma kasar Sin, an kammala wannan taro tare da yin kira da a lalata makaman nukiliya.

An dai samu wanzuwar kyakyawan yanayin siyasa da zaman lafiya tsakanin kasashen kungiyar, wadanda bisa al´ada suke da bambamcin tsare-tsare na zamantakewa da kuma manufofin siyasa. Tsofaffi da sababbin membobin sun ci-gaba da tafiyar da aikin kungiya duk da cewa ba ta da wata hedkwata ko wani tsarin mulki a hukumance. Shugaban kasar da ya karbi bakoncin shirya taron kungiyar ne shugabanta yayin da ministan harkokin wajenshi kuma ke tafiyar da aikinta tare da taimakon wani wakili na MDD.

Tun bayan rushewar TS kungiyar ta ´yan baruwanmu ta yi rashin wani angizo a siyasar duniya. In ban da kasashe masu matsakaicin ci-gaban masana´antu kamar Indiya da China, kusan dukkan membobin kungiyar su kimanin 114 na a jerin kasashe matalauta a duniya. Amma duka da haka suna biyayya ga dokokin kungiyar da kuma manufofinta. A saboda a bana kasar ATK ta gayyaci membobin kungiyar zuwa birnin Durban don halartar babban taron ministocinta daga yau wato 17 ga watan agusta zuwa 19 ga wata, don share fagen taron shugabannin kasashen Asiya da Afirka na biyu a shekara ta 2005, wanda zai yi daidai da taron koli na karo 14 na kungiyar kasashe ´yan baruwan mu wato shekaru 50 bayan taron kungiyar na farko a birnin Bandung.