1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin kasashen waje na Larabawa a birnin Alkahira

November 12, 2006
https://p.dw.com/p/BucN

Ayau ne ministocin harkokin wajen na kasashen Larabawa suka gudanar da wani taro na gaggawa a birnin Alkahiran kasar Masar,domin nazari kann taadin da Izraela ke cigaba dayi a yankin cin gashin kann Palasdinawa,musamman munanan kashe kashe da tayi a arewacin zirin gaza daya kashe palasdinawa fararen hula 18.Wannan taro na yau yazo ne,bayan da Amurka ta hau kujeran naki a komitin sulhun mdd adangane da kudurin yin Allah wadan hare haren na Izraela akan palasdinawa,wanda kasashen larabawan suka gabatar.

10 daga cikin kasashe 15 dake da kujera a komitin sun amince da kudurin,ayayinda sauran hudu da suka hadar da Britania da Denmark da Japan da Janhuriyar Slovakia ,suka ki halartan zaman.Anasaran Ministocin kasashen Larabawan,zasuyi nazari a dangane da yadda zaa bullowa wannan asaran rayuka da Izraelan ke cigaba da aiwatarwa Larabawan Palasdinun.