1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin ketare na KTT

July 17, 2006

Ministocin harkokin wajen kasashen KTT sun bayyana fargabar yaduwar rikicin gabas ta tsakiya domin zama ruwan dare a yankin

https://p.dw.com/p/Btz6
Farar hula a Lebanon
Farar hula a LebanonHoto: AP

Da yawa daga cikin ministocin harkokin wajen na kasashen KTT sun bayyana fargabar yaduwar rikicin domin zama ruwan dare a yankin baki dayansa. A cikin wata shawarar da aka zayyana dangane da sanarwar bayan taro an yi kira ga Isra’ila da tayi sara tana mai duban bakin gatarinta ka da ta nemi wuce gona da iri a matakai na soja da ta gabatar. Bai kamata kasar ta Isra’ila tayi fatali da yarjeniyoyi na kasa da kasa akan hakkin dan-Adam ba domin kuwa yin haka ba zai tsinana kome ba illa ya kara tsawwala mawuyacin halin da ake ciki duk da cewar tana da ‘yancin kare kanta. A daya hannun kuma shawarar sanarwar bayan taron tayi Allah waddai da kungiyar Hizballah tare da yin kira gare ta da ta saki sojojin Isra’ila guda biyu da take garkuwa da su ta kuma dakatar da hare-harenta akan garuruwan Isra’ila nan take. Ita kuwa gwamnatin Lebanon wajibi ne tayi bakin kokarinta wajen maido da dukkan al’amuran kasar karkashin ikonta ta kuma hana hare-haren kungiyar Hizballah. Bayan dawowarsa daga ziyarar da ya kai birnin Beirut, kantoman KTT akan manufofin ketare Javier Solana ya ce gwamnatin Lebanon karkashin jagorancin Fuad Siniora ta cancanci samun cikakken goyan baya dangane da wannan mawuyacin hali da kasar ta samu kanta a ciki. Muhimmin abu a yanzu shi ne hana yaduwar kurar rikicin domin zama ruwan dare a yankin gabas ta tsakiya baki daya in ji ministan harkokin wajen Jamus Franz-Walter Steinmeier. Shi ma ministan harkokin wajen kasar Sweden Jan Eliasson ya bayyana irin wannan damuwa musamman ma ganin cewar akwai dimbim ‘yan kasashen KTT dake zaune a wannan yanki. A dai halin yanzu daruruwan ‘yan kasashen ketare ke kokarin ganin sun fice daga Lebanon a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da ruwan bamabamai a sassa daban-daban na kasar sannan ita kuma kungiyar Hizballah tana mai mayar da martani ta kai hare-haren rokoki akan garuruwan Isra’ila. Amma duk da haka ana ci gaba da kokarin shawo kan rikicin a diplomasiyyance. Wakilin musamman na MDD Vijay Mambiar ya ce yana da niyyar gabatarwa da Isra’ila wata takamaimiyar shawara domin kawo karshen rikicin, bayan da suka gana da wakilan gwamnatin Lebanon a yau litinin. An kuma ji daga bakin sakatare-janar Kofi Annan yana mai fadin cewar:

“Na yi kira ga dukkan wadanda lamarin ya shafa da su yi wa Allah da Ma’aiki su kula da rayukan farar fula da kuma hanyoyin sadarwar dake da muhimmancin matuka ainun ga harkokin rayuwarsu ta yau da kullum. Bai kamata a kara tsawwala radadin da wadannan mutane ke fama da shi ba. Wajibi ne dukkan sassan biyu su girmama yarjeniyoyi na kasa da kasa akan hakkin farar fula.”

Ita dai kungiyar Hizballah ta ce faufau ba zata amince da sharuddan Isra’ila na sakin fursinonin da dakatar da hare-hare kan garuruwanta da kuma kwance damarar makamanta ba.