1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin kudi na G7

April 21, 2006
https://p.dw.com/p/Bv1F

Ministocin kudi da shugabannin bankuna daga kasashen duniya masu arzikin masaantu zasu gana a yau domin duba wasu batutuwa da suka shafi makamashi a duniya.

Kasar Amurka da kawayenta cikin kungiyar ta kasashe 7,zasu tattauna batun hauhawar farashin makamashi,batun yaduwar cutar murar tsuntsaye da illarta ga tattalin arzikin duniya, harkokin ciniki da saka hannayen jari da ka iya zama matsala ga ci gaban tattalin arziki a duniya.

Sauran kasashen kungiyar ta masu arzikin masaantu sun hada da Japan,Jamus,Faransa,Burtaniya,Italiya da Canada.

Kasashen Saudiya,Sin;Rasha,Australia da hadaddiyar daular larabawa,zasu shiga cikin wasu daga tattaunawar tasu.

Kasar Amurka dai zata yi kokarin ci gaba da matsawa kasar Sin sake duba manufofinta na kudi,wanda Amurkan take ganin yana da alaka da ja bayan harkokin ciniki na Amurkan.