1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU Finanzminister

November 17, 2010

Ministocin kudi na tarayyar Turai na yin nazarin ceto tattalin arzikin kasar Ireland

https://p.dw.com/p/QC82
Ministan kudin Jamus Wolfgang Schaeuble a zaune tare da takwarorinsa na kasashen EU yayin taron su a BrusselsHoto: picture alliance/dpa

A cikin jawabin da yayi shugaban hukumar kungiyar Taryyar Turai Herman von Rompuy cewa ya yi  ba ma ga kudin euro ne kadai matsalar tattalin arzikin da duniya ke fuskanta zata yi  mummunan tasiri ba . Za ta kuma yi tasiri ne ga baki dayan kungiyar tarayyar Turai. Su kuma a nasu bangaren wakilan kungiyar gargadi suka yi game da yi ma wannan alamar rikon sakainar kashi.

Ministocin kudin kungiyar sun yi wa kasar Ireland albishir da cewa ana tanadin wani asusu na musamman domin ceto ta daga duk wata matsalar kudi da za ta fuskanta. Shugaban wakilan kungiyar Klaus Regling yace za'a tanadi kudade cikin kwanaki biyar zuwa takwas a duk sanda kasar ta bukaci taimakon kudi.  To ama za'a ci gaba da tattaunawa tsakannin wakilan kungiyar tarayar turai da babban Bankin turai da  asusun ba da lamuni na duniya da kuma gwamnatin Ireland, akan kudin da kasar zata bukata da kuma yiwuwar samar da wannan kudi.

Irland Premierminister Brian Cowen
Firaministan Ireland Brian CowenHoto: AP

Ganin irin tasirin da daukar irin wannan mataki ke yi  akan bankuna ne kuma ya sa Josef Ackerman shugaban Deutsche Bank na nan Jamus yayi kashedi ga ministocin game da yaduwar wannan matsala zuwa sauran kasashe inda yace wajibi ne a samu hanyoyin dakile yaduwar wannan matsala. Yace akwai bukatar ceto duk wata kasa da ta tsinci kanta a cikin wannan hali. Acckerman ya fadi haka ne saboda fargabar da yake yi cewa mai yiwuwa ne bankunan su fuskanci karancin kudin da suke ba da su a matsayin rance.

Idan har wannan matsala ta shafi Jamus nan gaba banki mai zaman kansa ne ya kamata ya ceto ta amma ba masu biyan haraji ba. To sai dai Jean Claude Junker shugaban rukunin kungiyar Tarayar Turai, kwantar da hankalin Ackerman yayi da cewa nan da tsakiyar shekarar 2013 babu wani taimako da za'a nema daga wani banki mai zaman kansa domin daidata tattalin arzikin Girka da Portugal da kuma Irland .

A baya bayan nan sai da aka yayata jita jitar cewa wasu kasashen kungiyar Tarayar Turai da suka hada da Portugal da Spain sun yi kira ga Ireland ta shiga sahun kasashen dake neman taimako domin ceto tattalin arzikinta, abin da zai kwantar da rudani a kasuwanni.  Wolfgang Schäuble bai ba da takamammiyar amsa ba game da tambayar da aka yi masa cewa ko da wani matsin lamba.

To amma idan muka yayi la'akari da bukatar tandar kudi a dangane da wannan matsala za'a gano wannan wani mataki ne da ake dauka domin nuna dankon zumunci amma ba matsin lamba ba. To sai dai akwai fassara daban daban da za'a iya yiwa wannan mataki, saboda daukarsa da za'a yi tamkar taimako ko zumunci ko kuma mastin lamba. Kungiyar Tarayyar Turai ce kadai za ta iya fassara wannan mataki. 

Mawallafa : Christoph Hasselbach/Halima Balaraba Abbas

    Edita :     Abdullahi Tanko Bala