1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin kunɗin EU a Brussels

Sadissou YahouzaMay 9, 2010

Iya ruwa fidda kai:Ministocin kunɗin ƙasashen EU sun haɗu a Brussels domin tattana matsalar Girka , da kuma hana ɓullar ta zuwa sauran ƙasashen EU

https://p.dw.com/p/NJvA
Taron Ministocin kuɗin EU a Brussels

A yanzu haka ministocin kuɗi na ƙasashe membobin Ƙungiyar Tarayya Turai, na cigaba da zaman taro a birnin Brussels da zumar laluben hanyoyin ceto takardar kuɗin Euro daga barazanar kariyar darajar da take fuskanta  a halin yanzu, da kuma ɗaukar matakan riga kafi, na hana yaɗuwar matsalar tattalin arzkin Girka, ga sauran ƙasashen EU.

Wannan taron gaggawa  ya biwo bayan haɗuwar shugabanin ƙasashen EU, ranar juma´a da ta wuce a birnin Brussels, inda suka ɗauki alƙawarin aiki tuƙuru, domin kare ƙasahasen daga kariyar tattalin arziki.

Saidai ministan kuɗin Jamus , Wolfgang Schäuble dake halartar taron, ya fukanci motsuwar jiki, inda a yanzu yake kwace a wata asibitin Brussels.

Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi Edita: Umaru Aliyu