1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin Kungiyar EU a birnin Brussels.

YAHAYA AHMEDNovember 8, 2005

A ran litinin da ta wuce ne ministocin Kungiyar Hadin Kan Turai suka yi wani taron yini daya a Brussels, inda suka yi shawarwari kan batutuwa da dama da suka hada da rikicin da ake yi da Iran kan batun makamshin nukiliyanta.

https://p.dw.com/p/Bu4O
Hedkwatar Kungiyar Hadin Kan Turai a birnin Brussels.
Hedkwatar Kungiyar Hadin Kan Turai a birnin Brussels.Hoto: AP

Kungiyar Hadin Kan Turai, ta ce ta bai wa kasar Iran amsar wasikar da ta aike mata game da rikicin da ake yi kan batun makamshin nukiliyanta. Ministocin harkokin wajen kungiyar ne suka bayyana haka bayan wani taron yini daya da suka yi a ran litinin a birnin Brussels. A cikin sanarwar bayan taron da suka bayar, ministocin sun ce ba za su shuga cikin wani shawarwari da Iran din ba, sai kasar ta dakatad da shirye-shiryenta na azurta yurenium, sinadarin da ake gani zai ba ta damar sarrafa atam bam. Da yake yi wa maneman labarai jawabi, ministan harkokin wajen Birtaniya, wanda kuma shi ne ke shugabancin Kungiyar Hadin Kan Turan a halin yanzu, Jack Straw ya bayyana cewa:-

„Dole ne Iran ta kiyaye ka’idojin da Hukumar Kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ta shimfida mata. Muna dai sa ran za ta yi hakan.“

A cikin watan Satumban da ya gabata ne, Hukumar, wato IAEO a takaice, ta bukaci Iran da ta bayyana duk shirye-shiyenta na makamashin nukiliyan a fili. A makon da ya gabata ne dai Iran din ta ba da sanarwar cewa ta amince a gudandad da bincike kan wasu kafofinta na makamashin nukiliya, wadanda a da can wato sirri ne gareta. A cikin watan Agustan da ya gabata ne kuma, sabon shugaban kasar, Mahmud Ahamadinijad, ya ba da umarnin a ci gaba da azurta yureniyum a kafar nan ta Isfahan, abin da ya janyo fusatar Kungiyar Hadin Kan Turai har ta katse tattaunawar da take yi da mahukuntan birnin Teheran.

To bayan hakan ne, babban jami’in Iran a kan batun makamashin nukiliyan, Ali Larijani, ya aike wa kasashen Kungiyar Hadin Kan Turan guda 3, wadanda ke tattaunawa da hukumarsa, wato Birtaniya da Faransa da Jamus, wata wasika, inda ya gayyace su su sake zuwa kan teburin shawarwari su tattauna matsalar, amma ba tare da wani sharadi ba. Har ila yau dai, ba a fara tattaunawar ba tukuna. Amma Jack Straw ya bayyana cewa, duk da hakan, ana ta shawarwari bayan shinge da Iran din.

A halin da ake ciki dai, ana jira ne a ga shawarar da Hukumar IAEO din za ta yanke a zaman da za ta yi a ran 24 ga wannan watan, inda za ta tattauna batun makamashin nukilyan Iran din. A wannan ranar ne za a yanke shawarar ko a mika batun ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ko kuma a san yadda za a yi. Amirka da Birtaniya dai na neman a kai karar Iran gaban kwamitin. Amma Rasha na adawa da hakan.

A wata sabuwa kuma, ministocin Kungiyar Hadin Kan Turan, sun ce za su fadada kafofin wakilcinsu a yankunan Falasdinawa don hanzarta hidimomin da ake yi na samad da zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya.

Tun daga frakon shekara mai zuwa ne kungiyar ta ce za ta tura jami’ai 30 zuwa 50 a yankin don su horad da jami’an tsaron Falasdinawa a biranen Gaza da Ramallah. Kazalika kuma sun ce, za su girke jami’an sa ido kan iyakar Zirin Gaza da Masar a garin Rafah .

Game da batun kasafin kudin kungiyar kuwa, har ila yau dai ba a cim ma daidaito ba. Birtaniya ta dage kan kare rangwamín da take samu na Euro biliyan 5, daga gudummuwar da za ta dinga bai wa asusun kungiyar, yayin da Faransa kuma ba ta sha’awar ganin an tabo batun fa’idar da take samu na tallafin da ake bai wa manomanta daga kasafin kudin kungiyar.

Ministocin dai sun nuna rashin amincewarsu da bukatar ta Faransa, inda kuma suka bukaci kwamishinan ciniki na kungiyar, Peter Mandelson, da ya gabatar da wani shiri na rage tallafin da kungiyar ke bai wa manomanta, a taron kuingiyar Ciniki Ta Duniya da za a yi nan gaba. Sai dai, ita Faransan ta zargi kwamishinan da wuce gona da iri. Ta kuma yi barazanar hawar kujerar na ki, don soke duk wata shawarar da za a yanke a kan wannan batun, idan hukumar ta ci gaba da aiwatad da shirinta.