1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin kungiyar kasashe 8 masu tasowa

Hauwa Abubakar AjejeMay 11, 2006

Kungiyar kasashe 8 masu tasowa ta bude taronta yau a birnin Bali ba kasar Indonesia kafin babban taron shugabannin kasashen nan gaba cikin wannan mako.

https://p.dw.com/p/Bu0B
Ahmedinajad da Susilo Bambang na Indonesia
Ahmedinajad da Susilo Bambang na IndonesiaHoto: AP

A yau ministocin harkokin wajen kasashen,Bangladesh,Masar,Indonesia,Iran,Malaysia da Nijeriya da Pakistan da Turkiya suka bude taron share fage na babban taron shugabannin kungiyar kasashen takwas masu tasowa nan gaba a ranar asabar.

Wannan taro dai zaifi mayarda hankali ne akan batutuwa da suka shafi hadin kan ciniki da tattalin arziki,da kuma fannonin saka jari da kimiya da masanaantu.

Ana kuma sa ran batun nukiliya na kasar Iran zai mamaye taron,shugaban kasar Iran din zai halarci wannan taro,ana kuma sa ran zai bukaci kasar Indonesia,ta taka muhimmiyar rawa ta mai shiga tsakanin a rikicinsa na nukiliya da kasashen yammacin duniya.

Ahmedinajad wanda zai kuma tattauna akan batutuwa da dama a lokacin ziyarasa kafin taron shugabannin kungiyar kasashen 8,tunda farko ya baiyanawa kasashen yammacin duniya cewa,shirinsa na nukliya na anfaninsa na cikin gida ne,kodayake suna ganin cewa,kokari kasar ta Iran takeyi na kera makaman nukiliya.

Maaikatar harkokin wajen Indonesia,ta sanarda cewa,taron zai duba hanyoyin kare fadawa matsalar makamashi a duniya,inda zai tattauna hanyoyi daban na samarda makamashi da kuma jujjuya albarkarun makamashin,ciki har da makamashin nukliya.

Kasar Indonesia wadda zata karbi shugabancin kungiyar daga hannun kasar Iran,ta tsara wasu kudurori akan anfani da makamashin nukiliya cikin lumana,wadanda zaa tattauna akansu wajen taron na Bali.

Hakazalika wajen taron,zaa maida hankali akan hanyoyin karfafa cinikaiya,rage basusuka da kulla dangantaku a fannonin tattalin azriki tasakanin kasashen 8 masu tasowa.

Ministan harkokin wajen Indonesia Hassan Wirajuda,wajen taron ministocin kasashen a yau ya baiyanawa yan jarida cewa,zaa sanya hannu akan yarjeniyoyi 2 na ciniki tsakaninsu.

Taron na shugabannin kungiyar kasashe 8 masu tasowa a ranar asabar,zai samu halartar,Firaministan kasar Turkiya Racep Tayyip Erdogan,Firaminitan Pakistan Shaukar Aziz,Firaminsta Abdullah Ahmed Badawi na Malaysia da shugaba Olusegun Obasanjo na Najeriya.

Kasashen Masar da Bangladesh,ministocin harkokin wajensu ne zasu wakilce su.

Taron kungiyar ta kasashe 8 masu tasowa na farko ya gudana ne,a 1997,kuma taronta na baya tayi shine a birnin Tehran na kasar Iran a 2004.