1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin tsaro na ƙasashen EU

September 29, 2007
https://p.dw.com/p/Bu9y

Ministocin tsaro na ƙasashen ƙungiyar gamayya turai na ci gabada zaman taro a birnin Evora, na ƙasar Portugal.

A ranar farko ta wannan taro ,sun cimma daidaito a game da matakin aika rundunar shiga tsakani a ƙasar Tchad.

Ranar talata da ta wuce, komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia, ya kaɗa kuri´a amincewa da aika wannan runduna, domin taimakawa dubunan yan gudun jihira na yankin Darfur dake ƙasar Tchad, su koma matsugunan su.

Ƙungiyar EU ta alƙawarta tura dakaru dubu 3, a cikin wannan runduna, ya zuwa yanzu, tunni an samu a ƙalla sojoji dubu 2.

France ke da tawaga mafi girma wadda ta ƙunshi dakarau 1.500

ƙasashen Irland da Sweeden, sun alkwarta aikawa da sojoji , sannan da dama gada sauran ƙasashen EU sun ambata bada gudummuwa ta jirage da kayan aiki.

Saidai kasar Jmaus da ke matsayin kasa mafi karfinfada aji a cikin EU ta ce a halin yanzu, ba zata iya aika wata runduna ba a ƙetare.