1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin tsaro na ƙungiyar NATO a Netherlands

October 24, 2007
https://p.dw.com/p/C15k
Tabarbarewar halin tsaro da kuma kutsen da ´yan tawaye ke yi a Afghanistan shi ya fi daukar hankali a taron ministocin tsaron kungiyar kawance ta NATO dake gudana a kasar NL. Kasashen Amirka da Birtaniya na matsawa kawayensu na Turai lamba da su ba da karin dakaru da kayan aiki a yakin da ake yi ´yan tawayen Taliban a Afghanistan to amma majiyoyin kungiyar sun nunar da cewa kasashen biyu ba zasu samu yadda suke so ba. Ministocin na kuma tattaunawa akan shirin Amirka na kafa sansanonin kandagarkin makamai masu linzami a kasar Poland da Janhuriyar Czeck.