1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

TARON MINISTOCIN TSARON KUNGIYAR NATO A BIRNIN NICE - FARANSA.

Yahaya AhmedFebruary 10, 2005

Taron ministocin tsaro na kungiyar NATO da ake yi a birnin Nice na kasar faransa, yana jan hankullan masharhanta da dama, saboda wannan shi ne karo na farko da Faransan ta taba karbar bakwancinsa. Ministan tsaron Faransan ta ce ta na so ne ta bayyana cewa gwamnatinta ta dukufa wajen karfafa reshen kungiyar na nahiyar Turai.

https://p.dw.com/p/BvdC
Ministocin tsaron kungiyar kawance ta NATO, a taronsu na birnin NICE a kasar Faransa.
Ministocin tsaron kungiyar kawance ta NATO, a taronsu na birnin NICE a kasar Faransa.Hoto: AP

A taron kungiyar NATO da aka bude a birnin Nice na kasar Faransa, sakataren tsaro na Amirka, Donald Rumsfeld, ya sake nanata kiran da ya yi na neman duk mambobinm kungiyar, su ba da kaimi wajen horad da jami’an tsaron kasar Iraqi. Kazalika kuma Janar Sakatare na kungiyar Jaap de Hoop Scheffer, shi ma ya bayyana ra’ayin cewa, zaben da aka gudanar a Iraqin yana da muhimmanci kwarai. Sabili da haka, yana ganin wajibi ne ga kungiyar NATOn da ta dada ba da karin gudummuwa wajen horad da jami’an Iraqin.

A taron kolin kasashen NATOn da aka yi a cikin watan Yunin da ya gabata dai, kungiyar ta dau alkawarin tura malaman horon tsaro dari 3 zuwa birnin Bagadaza. Amma kawo yanzu, ba a cim ma wannan gurin ba. Shugaban rukunin horad da jami’an tsaron a Iraqi, Janar Petreus na Amirka, ya bayyana cewa ko da an sami malamai dari da 59 ma, da hakan zai wadatar wajen horad da jami’an tsaron Iraqi dubu a ko wace shekara. A halin da ake ciki yanzu dai, rahotanni sun ce kungiyar NATOn, malamai dari da 9 ne suka tura zuwa Iraqin.

D

aya daga cikin dalilan da suka janyo karancin masu ba da horon a birnin Bagadaza kuwa, shi ne daddagewar da wasu mambobin kungiyar, wato Faransa, da Jamus, da Spain, da Belgium ke yi na tura dakarunsu zuwa Iraqin, duk da angaza musu da Amirka ke yi. Game da hakan dai, ministan tsaron Jamus, Peter Struck, ya bayyana cewa, babu wani sabani da ake samu a bainar kungiyar. Ita dai gwamnatin tarayyar Jamus ta bayyana matsayinta dalla-dalla. Sabili da haka ne, take ba da tata gudummuwa wajen horad da jami’an tsaron Iraqin, amma ba cikin kasar ba.

Ita ko gwamnatin Birtaniya, ta dage ne kan cewa kamata ya yi, kasashen NATOn su kara yawan masu ba da horonsu a Iraqin. Tana kuma niyyar bayyana hakan din bisa manufa, a lokacin taron kolin kungiyar da za a yi a birnin Brussels a cikin kwanaki 10 masu zuwa nan gaba. Sai dai, kasashen Turan da dama na dari dari, da wannan matakin da Birtaniya ke ta kokarin angaza su su dauka. A ganin galibin kasashen dai, halin tsaro a Iraqin, wata kasada ce garesu, musamman idan aka zo ga batun kara tura yawan jami’ai.

An dai dauki tsauraran matakan tsaro a gun taron na birnin Nice. Jiragen yake na girke a gabar tekun birnin da shirin ko ta kwana. Kazalika kuma, jiragen sama masu saukar ungulu na ta shawagi ba kakkautawa a kan birnin. An kuma hana duk motoci kai-kawo a tsakiyar ma gaba daya.

Kamar dai yadda wata jaridar birnin "Nice-Matin" ta rubuta a cikin sharhinta, mazauna birnin dai sun ji ne kamar an yi musu kawanya.