1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin wajen kungiyar taraiyar turai

Hauwa Abubakar AjejeJanuary 22, 2007

Taron ministocin harkokin wajen kungiyar taraiyar turai ya bada goyon bayansa ga kafa takaitaccen takunkumi akan Iran game da shirinta na nukiliya tare kuma da yin Allah wadai da ci gaban kashe kashe a yankin Darfur na kasar Sudan.

https://p.dw.com/p/BtwX
Hoto: AP

Taron na KTT mai membobi 27,karkashin shugabancin ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Sreinmeier ya lashi takobin kaddamar da dukkan jerin takunkumi da komitin sulhu na MDD ya kafa kan kasar Iran saboda jajircewa da tayi game da shirinta na nukiliya.

Sun kuma yi kira ga dukkanin kasashe da suma su kaddamar da wannan takunki akan Iran,domon a cewarsu tilastawa Iran din ta koma teburin tattauna batun nukiliyar tata.

Kungiyar ta turai tace akwai yiwuwar fara aiki da takunkumin a farkon watan fabrairu mai kamawa,inda jamian kungiya suka baiyana cewa tuni sun fara tsara yadda takunkumin zai fara aiki,wanda ya hada da haramta sayarda fasahohin kimiya da danyun sinadarai da Iran zata iya anfani dasu wajen kera makaman atom.

KTT ta kuma yi alkawarin dakatar dukkan wata muamala da wadanda suke da hannu cikin shirin nuliya na Iran tare da dakatar da dukkan kadarorinsu dake waje.

Iran din dai a nata bangare tace wannan takunkumi ba zai hana ta ci gaba da shirin nata ba.

Ministocin harkokin wajen na tura sun baiyana fatar sake gina dangantaka da kasar Serbia biyowa bayan zabe da aka gudanar a karshen mako wanda ya baiwa masu goyon bayan demokradiya nasara.

Ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier yace sunyi maraba da wannan nasara ganin cewa kashi biyu bisa uku na kujerun majalisa zai tafi ne ga masu hankoron kasa demokrtadiya a kasar,yana mai alkawarta goyon bayan KTT ga kasar ta Serbia.

Minstocin har way au sunyi Allah wadai da karya dokokin yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Darfur suna masu baiyana ci gaban goyon bayansu ga dakarun AU tare ci gaba da matsawa Sudan lamba ta amince da aikewa da dakarun MDD zuwa yankin.

Komishin kula da ci gaba na KTT Louis Michel ya baiyana aniyarsa ta zuwa babban taron AU nan gaba cikin mako mai zuwa a Sudan tare da nufin janyo hankalin shugabanin Sudan su amince da dakarun na MDD.

Kodayake Michel yace basu da isassun kudi da ake bukata na fadada aiyukan dakarun na AU sai dai kuma kasashen Nethrlands da Burtaniya sunyi tayin kara taimakon kudi ga aiyukan na darfur.

Ministocin hatkokin wajen na turai sun kuma rook gwamnatin Somalia data shiga tattaunawa da dukkannin bangarorin kasar ciki har da shugabanin islama masu sassaucin raayi domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a kasar.

Louis Michel na kungiyar yace rashin tattauna da dukkan bangarorin siyasa na kasar zai ruguza kokari da akeyi na kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar da take cikin kangin talauci.

KTT ta kuma yi Allah wadai da sauke kakakin majalisar Somalia Sharif hassan Sheiik Aden,suna masu cewa yin hakan zai shafi harkokin sasanta bangarorin kasar,ganin cewa Aden zai iya janyo hankalin wasu shugabannin kungiyoyin islama cikin tattaunawar.