1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron muhawara don yiwa majalisar dinkin duniya garanbawul

August 31, 2005

Wakilan Majalisar dinkin duniya na tattaunawa a kan daftarin shawarwarin yiwa majalisar kwaskwarima.

https://p.dw.com/p/Bva5
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kofi AnnanHoto: AP

Jakadun majalisar dinkin duniya na cigaba da muhawara domin cimma daidaito a kann wasu muhimman batutuwa wadanda zaá gabatarwa babban taron majalisar a watan Satumba don yiwa majalisar garanbawul. Shi kan sa babban sakataren majalisar Kofi Annan a jiyan ya sanke hutun da yake yi a mahaifar sa kasar Ghana ya dawo inda ya koma hedikwatar MDD domin tantance irin cigaban da ake samu a shawarwarin yiwa majalisar garanbawul. Wakilan wani muhimmin kwamiti da ya kunshi mutane 33 ya dukufa ba ji ba gani domin gano bakin zaren warware sabanin da ake da shi akan wasu muhimman kudire kudire guda bakwai kafin ranar 14 zuwa 16 ga watan na satumba da zaá gudanar da taron majalisar.

A yanzu haka shugaban babban zauren majalisar Jéan Ping yana jagorantar shawarwarin da ake fatan zasu kai ga samun masalaha yadda baki zai zo daya a game da batun yiwa majalisar gyaran fuska, Ana fatan mika shawarwarin da jakadun suka cimma ga taron shugabannin kasashe na duniya domin amincewar su. Muhimman batutuwan da suka fi daukar hankali wadanda kuma ake tafka muhawarar akan su sune taáddanci da bunkasar cigaba da kawar da rage yaduwar muggan makamai da hakkin kare rayuwar mutane daga barazanar kisan kiyashi da daftarin kwaskwarimar majalisar da farfado da karfin ikon majalisar lura da kare hakkin bil Adama da kuma hukumar kiyayen zaman lafiya ta duniya. A game da batun taáddanci da kafa hukumar kiyaye zaman lafiya ta duniya don taimakawa kasashen dake fama da rikice rikice, an kafa wani karamin kwamiti da zai bi didigi da tattara bayanai a game da batutuwan guda biyu.

Wakilan taron sun kuma maida hankali a game da nauyin da ya rataya a wuyan majalisar na kare hakki da kuma rayuwar mutanen da ka iya fuskantar barazana ta kisan kare dangi, a nan ma an kafa wani karamin kwamiti da zai tsara daftarin shawarwari a wannan bangaren. Jakadan kasar Amurka a majalisarr dinkin duniyar John Bolton ya shaidawa yan jarida cewa zaá yi gumurzu a yan makwanni masu zuwa, to amma yace zaá sa ido a ga yadda lamarin zai kaya. Taron na watan gobe sakataren majalisar dinkin duniyar Kofi Annan shi ne ya bukaci gudanar da shi domin nazarin irin cigaban da aka samu a shirin raya kasashe ma Millenium goal wanda aka samar da shi shekaru biyar da suka gabata sannan kuma da rattaba amincewa da garanbawul din majalisar a karon farko tun kafuwar ta shekaru sittin da suka wuce.

A makon da ya gabata John Bolton ya tabo batun da ya sosawa wakilai daga kasashe masu tasowa rai musamman a game da batun raya cigaban kasashe. Jakadan na Amurka ya matsa da a soke dukkan sashe da ya ambaci shirin na Millenium goal wanda wakilan majalisar suka tsayar da cewa a karkashin shirin ana fatan kakkabe talauci da cutattuka a kasashe matalauta nan da shekaru goma sha biyar masu zuwa. A hannu guda dai sakataren majalisar dinkin duniyar Kofi Annan tare da mafi rinjayen wakilan majalisar na goyon bayan shirin na Millenium goal wanda ya sami karbuwa daga al´momi da dama na duniya. A game kuwa da kafa majalisa wadda zata kula da kare hakkin bil Adama domin maye gurbin hukumar kare hakkin dan Adam ta majalisar, Jakadan kasar Pakistan Munir Akram yace har yanzu ba kai ga cimma shawarwari ba a game da yadda sabuwar majalisar zata kasance da ayyukan ta da kuma cancanta da yanayin zaben wakilan da zasu yi aiki a cikin ta. A baya dai an zargi hukumar kare hakkin bil Adaman da nuna wariya inda ta fi mayar da hankali akan kasashe masu tasowa da cewa sune suka fi take hakkin dan Adam. Kofi Annan ya bada shawarar rage yawan wakilan hukumar kare hakkin bil Adaman ya zuwa rabin adadin wakilan ta na da sannan a zabo sabbin wakilan bisa laákari da matsayin su na kare hakkin bil Adama. Shawarar ta biyo bayan zargin da ake wa hukumar da cewa cike take da wakilai da kasashen su suka yi kaurin suna wajen take hakkin dan Adam.