1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Munich kan Siriya ya cimma matsaya

Abdourahamane HassaneFebruary 13, 2016

Sai dai kuma duk da haka rundunar mayaƙa sama ta Siriya da ke samun goyon bayan Rasha ta ci gaba da buɗe wuta a yankuna da ke cikin hannu 'yan tawayen.

https://p.dw.com/p/1HumW
München Sicherheitskonferenz Rede Adel al-Dschubeir Saudi Arabien Außenminister
Hoto: DW/A. Feilcke

An ba da rahoton cewar dakarun gwamnatin Siriya sun ci gaba da buɗe wuta awowi kaɗan bayan da taron da ake yi a birnin Munich na ƙasashen duniya,da nufin kawo ƙarshen tashin hankali ya cimma wata yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta.

Ƙungiyoyin kare hakin bil Adama sun ce aƙalla an kashe faran hula 16,a yankunan da 'yan tawayen suka ja daga.Amirka dai ta yi kira ga shugaba Bashar Al Assad da cewar ya yi hattara samakon furcin da yayi a jiya, cewar dakarunsa da ke samun goyon bayan Rasha za su ci gaba da yaƙi har sai sun ƙwato sassan ƙasar baki ɗaya daga hannun dakarun 'yan tawayen.