1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron musulmin Jamus da wakilan Gwamnati

Zainab MohammedMarch 14, 2008

Ƙaddamar da darasin addinin Islama a makarantun Jamus

https://p.dw.com/p/DOUS
Ministan cikin gidan Jamus Wolfgang Schaeuble da kakakin majalisar Musulmi Bekir Alboga.Hoto: AP

Tattaunawar zamantakewa tsakanin musulmi dake zaune a tarayyar Jamus da gwamnati ba wani sabon batu bane,sai dai a karo na uku na ire-iren waɗannan tarurruka da aka gudanar a jiya,an jaddada bukatar sanya koyarda addinin islama cikin jadawalin makarantu da 'yancin gina masallatai da karin haɗin gwiwa tsakanin musumin da hukumomin tsaro.

An gudanar da irin wannan taro a karon farko nedai a watan Satumban shekarat 2006,wanda ya haɗar da mahawara tsakanin gwamnatin tarayyar jamus da wakilan musulmi kimanin million 3 da dubu ɗari 2 dake zaune a sassa daba-daban na ƙasar.

Wannan irin taro dai nada nufin mahawara kan kyakkyawar zamantakewa tsakanin musulmin da sauran alummomi,da kuma yadda za a tattauna wasu batutuwa da suka shafi rayuwar dukkannin alummomin.

A karo na ukun wannan taro daya daya gudana jiya a birnin Berlin dai,wanda ya samu halartan wakilan gwamnatocin jihohi dana tarayyara akarkashin jagorancin ministan harkokin cikin gida Wolfgang Schaüble dai, an gabatar da muhimman batutuwa da suka shafi rayuwar mulmin dake nan tarayyar jamus.

Shaeuble ya ɗora alhakin tabbatar da fahintar juna a zamatakewa da sauran jama'a a wuyan taron haɗin gwiwar.Da kafa wannan taro watanni 18 da suka gabata dai,an kafa kungiyoyi guda hudu wadanda zasu aiki domin tabbatar dacewar an ingata zamantakewa da fahintar juna tsakanin musulmi sama da million uku dake wannan kasa,wadanda rabinsu Turkawa ne.

Duk dacewar ya amince da saɓanin dake da akwai tsakanin ɓangarorin biyu,Ministan cikin gidan na jamus yace wannan ba wata babbar matsala bace..

"Yace a yanzu munyi mahawara na tsawon saoi hudu,kuma mun tattauna muhimman batutuwa.Sai dai har yanzu muna bukatar dada sanya himma,akan wannan taro na musulmi,musamman a bangaren kungiyoyin dake aikin tabbatar da fahintar juna,saboda ya zamanto wajibi akansu su sauke wannan nauyi da aka dora musu".

Ministan harkokin cikin gidan jamus din dai yayi fatan cewar kaddamar da koyar da ilimin addinin islama a makarantu zai taimakawa yara musulki fahintar addinin sosai tare da rage yawan masu tsattsauran ra'ayi wadanda ya danganta da hudubobin da akeyi acikin masallatai.

"Ko wace ƙasa tana muradin cimma manufofin kyakkyawar zamantakewa dangane da bukatun addinai,dayake kowace jiha tana da yadda take gudanar da harkokin ta mulki,kowace nada ikon kaddamar da koyar da ilimin addini.Dole ne a tuntubi iyayen yara an kuma tattauna dasu,idan sun bayyana bukatar haka ,babu wata matsala gwamnati zata tsara,kuma jihohin kasar da yawa ma na iya aiwatar dashi a makaranzunsu"

Wata baturkiyya marubuciya mai kula da harkokin rayuwa Necla Kelek kuma daya daya cikin mahalarta taraon tana mai raayin cewar.

"Tunda zamu aiki tare kan waɗannan batutuwa da muke bukata,a bangare na wannan babban cigaba ne ,koda yake wannan batu yabar kofofi da dama na ayar tambaya...".

Kakakin majalisar musulmi dake nan tarayyar Jamus Bekir Alboga ya bayyana kaddadamar da koyar da addinin musulunci a makarantu da kasancewa wani babban mataki ne na cigaba.

Shima Bishop Wolfgang Huber,yayi maraba da wannan batu sai dai ya jaddada bukatar daukar malamai sanannu waɗanda zaa dorawa wannan alhaki.