1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron nazarin yankunan karkara

June 19, 2007

An gabatar da taro na biyu akan matakan yankunan karkara na kasashe masu tasowa a birnin Berlin

https://p.dw.com/p/BtvJ
Wieczorek-Zeul
Wieczorek-ZeulHoto: AP

Taron dake samun halarcin wakilai 350 da suka hada da jami’an siyasa da jami’an taimakon raya kasa na kafofin KTT da kungiyoyi masu zaman kansu da kuma kwararru daga kasashen dake samun taimakon zai zo karshensa ne a ranar alhamis mai zuwa. Babban abin da za a mayar da hankali kansa shi ne nagartattun matakai masu dorewa don raya yankunan karkara, musamman a kasashen Afurka. A dai halin da muke ciki yanzu haka kimanin kashi uku bisa hudu na al’umar duniya sun dogara ne kacokam akan ayyukan noma, amma da kyar ne suke iya samun wadataccen kayan masarufi na yau da kullum. A jawabinta na bude taron, ministar taimakon raya kasashe masu tasowa ta Jamus Heidemarie-Wieczorek-Zeul tayi nuni da cewar:

“Har kwanan gobe noma zai ci gaba da taka muhimmiyar rawa a yankunan kaerkara na Afurka. Kimanin mutane miliyan dari biyar ke dogaro akan noma. Wato ke nan muhimmancinsa a garesu ba sai an fada ba. Akwai bukatar tafiyar da ayyukan noman bisa wani nagartaccen tsarin da ya dace kuma wannan shi ne ainifin kalubalen da zamu fuskanta.”

Ministar taimakon raya kasar ta Jamus tayi nuni da cewar barin mutum da yunwa wani bangare ne na take hakkinsa a saboda haka ya zama wajibio a inganta hanyoyin noma a kasashen da lamarin ya shafa. N’Diogou Fall mai wakiltar wasu kungiyoyin manoma 12 daga kasar Senegal yana daga cikin masu halartar taron na Berlin, to sai dai kuma ya ce tuni ya fid da kauna game da cewar taron zai haifar da wani sakamako na kirki. Domin kawo yanzu dukkan yarjeniyoyin tattalin arzikin da ake kullawa zaka tarar KTT na wa kasashen Afurka matsin lamba domin su ba wa manoma na Turai damar shigar da rarar amfanin da suke nomawa a kasuwannin Afurka. Fall ya ce:

“Muna suka da kakkausan harshe a game da cewar ajendar taron bata kunshi tattauna ainihin matsalar dake dada jefa ayyukan noma cikin halin kaka-nika-yi a nahiyar Afurka ba. Domin kuwa ainifin matsalar ta siyasa ce, wadda ta tanadi manufofin ciniki ta bude kofofin kasuwanni da gasa tsakanin manoma na kasashe masu tasowa da takwarorinsu na kasashe masu ci gaban masana’antu dake tu’ammali da fasahar noma ta zamani.”

A cikin wata sanarwar da suka bayar wasu kungiyoyi na manoma da makiyaya na Afurka da Asiya da Latin Amurka sun bayyana cewar muhimmin abu shi ne duk wani matakin da za a dauka kada ya kasance mai barazana ga makomar kananan manoma. Wadannan kungiyoyin sun tsara nasu shirin a game da raya yankunan karkara da suke da niyyar gabatarwa a zauren taron.