1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron neman kyautata kasuwanci tsakanin Najeriya da Nijar

Ubale MusaAugust 13, 2015

A yunkuri na kyautata harkar kasuwancin kasashen makwabtaka, ana wani taron duba yiwuwar sauya akalar 'yan kasuwa da shigo da kayayyakin Jamhuriyar Nijar ta tashoshin jiragen ruwan Tarayyar Najeriya.

https://p.dw.com/p/1GFFk
Niger Buhari Issoufou
Hoto: DW/M. Kanta

A wani abun dake zaman sabon yunkurin kyautata harkar kasuwanci a tsakanin kasashen Najeriya da Nijar dake makwabtaka, an fara wani taron duban yiwuwar sauya akalar yan kasuwa da gwamnatin ta Jamhuriyar Nijar wajen shigo da kayyayakinta ta tashoshin jiragen ruwan Tarrayar Najeriya da nufin amfanin juna.

A baya dai dangantakar tafi maida hankali ga kokarin tabbatar da tsaro a tsakanin makwabtan kasashen masu dogon tarihi. To sai dai kuma sauyin shugabancin Tarrayar Najeriya na neman jawo rikidewar harkar ya zuwa ta kasuwa, inda yanzu haka yan kasuwa da jami'ai na gwamnatin Jamhuriyar Najriyar din ke nan Abuja suna nazarin yiwuwar komawar safarar hajjojinsu ta tashoshin jiragen ruwan Tarrayar Najeriya maimakon na Cotonou da Lome da Accra.

Wani taron dake can yana gudana a tsakanin jami'an kasashen biyu dai na nazarin hanyoyin kaucewar matsalolin rashin tsaro da matsi na jami'an da suka kori yan kasuwar na Nijar daga amfani da tashoshin dake zaman mafi kusa a garesu ta hanyar sufuri.

Tuni dai a kokarin biya masu bukata Najeriyar ta kara yawan cibiyoyin shigi da ficin dake kan iyakoki daga 14 da suke a baya ya zuwa 24 domin kara saukaka harkokin shigi da fici kan iyakar kasashen biyu mai tsawon kilomita 1500. 'Yan kasuwar ta Nijar dai na shigar da akalla ton miliyoyi da yawa na hajja daban daban a fadar Alhaji Idi Hamisu dake zaman jami'in ma'aikatar fitar da kayyayakin kasashe na Nijar a birnin Legos.

Niger alltägliche Straßenszene in Maradi
Saye da sayarwa a NijarHoto: picture-alliance/ZB

Babbar matsala dai a tunanin Ibra Abdu Kwalli, dake zaman daya a cikin yan kasuwar da ya hallaci taron na Abuja, dai na zaman aiyyuka na barayin da suke tare hanyoyi, da ma jami'an tsaro dake karbar hanci, sannan da bata lokaci a lokaci na fitar da kaya a tashoshin, matsalolin kuma da in an kai karshensu to a shirye yake game karfafa harkokin ciniki da kasuwanci tsakanin kasar ta Nijar da Najeriya.