1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron neman matakan shinfida zaman lahia a nahiyar Afrika

Yahouza sadissouSeptember 27, 2005

Jiya ne a birnin Paris na kasar Fransa, wakilan kasashe 40 daga nahiyoyin Afruka da turai, da kuma kungiyoyin kare hakokin bani adama, su ka shirya zaman taro, domin tantana matakan shinfida zaman lahia, a kasashen Afrika.

https://p.dw.com/p/BvZO
France
FranceHoto: AP

Wannan taro ,da shugaban kasar Fransa, ya gayyata, ya maida hankali, a kan wani tsarin cudayya ta fanin harakokin tsaro da Jacques Shirak ya kirkiro tsakanin Afrika da Turai.

Babban burin da ake bukatar cimma, ya shafi tabbatar da zaman lahia, a kasashen Afrika, masu fama da yake yake, da kuma riga kafi ga barazanar ta´adanci da ta fara zama ruwan dare a dunia.

Tsarin da Fransa ta sawa suna Recamp, ya gayyaci mahalarta taron, da su bayyana ra´ayoyi, a game da yiwar cimma burin da a ka sa gaba.

Kasashen da su ka halarci taron, sun hada da Afrika ta kudu Nigeria, Gabon, Cyadi, Angola, Jjamhuriya Afrika ta tsakiya, Kamaru, da dai sauran su.

Haka zalika, akwai wakilta, daga kasashen Amurika, da Kanada da kuma kungiyar gammaya turai.

Shugabanin taron, sun bayana bukatar su, ta kitsa dangata ta kut da kut, tsakanin su, da kungiyoyin taraya Afrika, ga gammaya, domin gama karfi, don samun cikkar nasara.

A daya hannun fussahar Recamp, na dauke da burin bada horo, ga dakarun rundunonin kasashen Afrika domin basu illimi da hussa´o´i, ta fanin lakantar ayyukan tsaro a kasashen Afrika.

Wannan taro, ya gudana a lokacin da kasar Fransa ke fuskantar barazanar hare haren ta´adanci, kamar dai yada ministan cikin gida, Nikolas Sarkozy ya bayyana jiya, a yayin da ya ke gabatar da sabin matakan da opishin sa, ya bullo da su, domin yakar ta´adanci, da kuma yi masa riga kafi.

Sarkozy ya sanar cewa, a ko da ya yawshe, akwai yiwuwar kai hare haren ta´adanci a kasar Fransa.

Daga jerin matakan da misnistan na cikin gida ya bayyana, akwai karffafa na´urori masu daukar hoton Video, na dukan abubuwan da ke wakana, a cikin birane da kawukka, inda ta wannan fannin, a cewar sa, an tsera wa kasar Fransa.

Haka zalika, akwai bukatar karfafa kulla da labaran da ke shiga da fita ta hanyoyin sakwanin yanar gizo-gizo, da na wayar talho.

A daya hanun kuma, Nikolas Sarkozy, ya tabatar da cewa, zai shiga kafar wando guda, da dukkan mutanen da su ka fito kara kara, a hili suna begen ayyukan ta´adanci, ko kuma suna kiran mutane tuwa ga wannan haramtattun ayyuka.

Ya ce tun daga shekara ta 2003, yan tsawtsawran kishin addinin Islama 34 ne, daidai Fransa ta kora, kuma a halin yanzu za a matsa kaimi ga hakan, domin a yanzu haka, akwai masu wa´azi zazzafa, kimanin 10 da jami´an tsaro su ka sawa ido.

Hata a ranar jiya jami´an yan sanda, sun binciko wata makarkasiya ta kai hare hare.

A samamen da su ka kai sun capke wasu mutane 9, yan kungiyar Jihadi ta GSPC dake Algeria, mai alaka da Alqa´ida.

Saidai basu gano ba, wata cikkar shaida, mai bayyyana cewa a zahiri mutanen su na shirin kai hari.

Duk da haka, jami´an tsaron sun yi awan gaba da su, da kuma littatafai, da na´urorin Computer masu yawa, domin ci gaba da bincike.